Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina

Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina

- Sai da muka biya naira miliyan 6.6 sannan aka sako yaranmu, cewar daya daga cikin iyayen yara 26 na jihar Katsina, inda suka bayyana gaskiyar lamarin

- Kamar yadda labarai suka yi ta yawo, cewa gwamnatin jihar Zamfara ce ta sasanta da masu garkuwa da yan mata 26 din nan, ashe ba gaskiya bane

- A cewarsu, gwamnatin jihar Zamfara ta gayyacesu gidan gwamnatin jihar, tukunna tace sai da ta saka baki tukunna aka saki yaran, duk da sun san ba haka bane

Wasu daga cikin 'yan mata 26 'yan karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, sun bayyana yadda ta kaya tsakaninsu da wadanda suka yi garkuwa da su.

Yaran da aka yi garkuwa da su daga gidajensu a ranar 13 ga watan Oktoba kuma aka sako su a ranar 3 ga watan Nuwamba sun sanar da gaskiyar magana a kan biyan naira miliyan 6.6 ga masu garkuwa da mutane.

Yayin da gwamnati tayi ikirarin cewa 'yan ta'addan sun sako su ne saboda ta saka baki kuma ta sasanta da su.

Jaridar Daily Trust ta tattauna da 'yan matan da al'amarin ya faru da su, inda suka ce sun biyo ta daji a kafa, an yi musu fyade babu iyaka.

A cewar daya daga cikin 'yan matan, 8 ne kacal daga cikin 'yan mata 26ne ba a yi musu fyade ba.

Kamar yadda tace, "Mun yi ta tafiya da kafafunmu na kwana 3. Idan dare yayi, sai su sama mana wurin da zamu kwana cikin dajin, mu cigaba da tafiya washegari.

"Muna tafiya ne har cikin dare, har sai mun jigata. Sun yi ta yunkurin kashe mu, domin mun sha duka, masu karfin halin cikinmu ne suke bamu kwarin guiwar cigaba da tafiyar.

"Sun yi wa da yawanmu fyade sau shurin masaki a cikin kwanakin nan.

"Wadanda ba su yi wa fyade ba kuma su kan sha duka, a kalla sau 10 duk dare."

Daya daga cikinsu har cewa tayi, bayan an sakosu, sai da aka yi mata karin jini saboda azaba.

A cewar wani Muhammad Adamu, daya daga cikin dattawan anguwar, sai da suka tura wa 'yan ta'addan naira miliyan 2.1, tukunna suka bukaci kari.

Sun bukaci su kara musu N400,000, bayan sun amsa suka bukaci karin naira miliyan 1.7.

Bayan an sakesu, gwamnatin jihar Zamfara ta gayyacesu, sannan aka ce musu sai da gwamnati ta saka baki tukunna aka sako yaran, sannan duk wanda ya tambayesu su ce kwana 5 yaran suka yi a hannun 'yan ta'addan.

KU KARANTA: An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas

Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina
Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan jihar Kaduna za su fara biyan harajin 1,000 a kowacce shekara, KADIRS

A wani labari na daban, kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun, ta yanke wa wasu mata 2, Suliyat Tajudeen da Ayomide Abdulazeez, hukuncin dauri a gidan yari bisa laifin yunkurin kashe gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, da sunan zanga-zangar EndSARS.

An yanke musu hukunci bisa laifuka da dama, ciki har da yunkurin kisa, makirci, lalata dukiyoyi da barna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel