Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta umarci dadironta

Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta umarci dadironta

- Wata budurwa da ke dadiro da wani mutum mai aure ta nemi ya saki matarsa, ya aureta

- A cewar budurwar, matar saurayin nata ta hanasu rawar gaban hantsi da more duniyarsu da tsinke

- Sai dai, magidancin ya ce ba zai iya barin matarsa da 'ya'yansa haka siddan, babu wani dalili ba

Wata fusatacciyar mata ta wallafa hirar da ta wakana tsakanin mijinta da farkarsa wadda ta take son ya bar matarsa ta sunna don a ƙulla igiyar da ita.

Mijin, wanda ya ke cutar matarsa, ya daɗe ya na neman hanyar da zai rabu da ita don ya auri farkarsa.

Zaku iya ganewa idanunku irin wainar da ake toyawa daga ɗaukar hoton sikirin da akayi.

Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta
Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta @Thenation
Asali: Twitter

Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta
Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta @Thenation
Asali: Twitter

Farkar ta yi wa abokin burminta ƙorafin cewar matarsa ta hanasu rawar gaban hantsi da cin duniyarsu da tsinke, inda ta bayyana cewa ba za ta cigaba jurewa ba.

Daga nan ta bashi wa'adin kwana bakwai akan ya bar ƴaƴansa da matarsa da duk ahalinsa, ya aureta don su cigaba da zama tare cikin farin ciki.

KARANTA: Matashin da ya yi takarar shugaban kasa a 2019 ya yi zargin cewa FG na neman rayuwarsa

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama tare da gurfanar da wani magidanci, Fahad Ali, bisa zarginsa da yin garkuwa da diyarsa, mai shekaru hudu, tare da neman N2m a matsayin kudin fansarta daga wurin matarsa, mahaifiyar yarinyar.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotun majistare da ke sansanin alhazai cewa mahaifiyar yarinyar ce ta fara sanar da rundunar 'yan sanda cewa an sace diyarta tare da yin garkuwa da ita.

Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta
Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta gayawa dadironta
Asali: Twitter

A cewar dan sandan, mahaifiyar yarinyar mai suna Shamsiyya Mohammed ta shaidawa rundunar 'yan sanda cewa wanda ya sace diyarta ya kirata a waya tare da neman miliyan biyu a matsayin kudin fansar diyarta.

Shamsiyya ta ce babu dadewa da sace yarinyar, a ranar 29 ga watan Satumba, ta samu kiran waya tare da sanar da ita cewa ko ta biya kudin fansa miliyan biyu ko kuma a kashe yarinyar.

KARANTA: INEC ta saka ranar gudanar da zabukan maye gurbi guda 15 a jihohi 11

Sai dai, bayan rundunar 'yan sanda ta shafe sati biyu ta na gudanar da bincike, ta gano cewa mijin Shamsiyya, Fahad Ali, shine ya yi garkuwa da yarinyar, wacce aka samu tare da shi.

Bayan an gama karanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu, Fahad ya ce shi sam bai aikata wani laifi ba.

Alkaliyar da ta saurari shari'ar, Sakina Aminu, ta bayar da umarnin a tsare Fahad a gidan gyaran hali har zuwa ranar, 24 ga watan Nuwamba, da za'a cigaba da sauraron karar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel