Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna

Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna

- Wata kotun majistare ta tura wasu mata 2 gidan gyaran hali da ke Ilesa a jihar Osun

- Ana zarginsu da yunkurin kashe gwamnan jihar da sunan zanga-zangar EndSARS

- Duk da har yanzu basu amsa laifin da ake tuhumarsu da shi ba, za a cigaba da bincike a kai

Kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun, ta yanke wa wasu mata 2, Suliyat Tajudeen da Ayomide Abdulazeez, hukuncin dauri a gidan yari bisa laifin yunkurin kashe gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, da sunan zanga-zangar EndSARS.

An yanke musu hukunci bisa laifuka da dama, ciki har da yunkurin kisa, makirci, lalata dukiyoyi da barna.

Dan sanda mai gabatar da kara, John Idoko ya ce wadanda ake zargi, masu shekaru a kalla 20, sun yi fashi da sata a Osun Mall da yake a Osogbo.

Idoko ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 17 ga watan Oktoban 2020 wuraren karfe 4:30 na yamma a Olaiya junction, a Osogbo.

A cewarsa, sun yi yunkurin kashe gwamnan jihar, ta hanyar amfani da bindiga da duwatsu suna jifansa. Sannan sun saci kayan da kimarsu ta kai N3,568,000, na wani Ashiru Ibrahim Olayemi.

Duk da wadanda ake zargin, sun musanta faruwar lamarin a kotu, lauyansu, Nurudeen Kareem, ya nemi belinsu, Daily Trust ta tattaro.

Amma alkalin kotun ya ki amincewa da bayar da belin, inda yace idan ba a hukuntasu ba, za su maimaita laifinsu.

Alkalin kotun, Olusegun Ayilara ya tura su gidan gyaran halin Ilesa har zuwa ranar 20 ga watan Nuwamban 2020.

KU KARANTA: Duba garejin dan wasan kwallo Obafemi Martins, mai dauke da kasaitattun motocin kece raini

Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna
Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma

A wani labari na daban, an damki wanda ya hada bidiyon bogi na auren minista Sadiya Umar Faruk da shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Janairu. An gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin hada bidiyon bogi.

Bayan zurfafa bincike, Hukumar DSS ta samu nasarar damko Kabiru Mohammed tun watan Janairu, amma bata gurfanar dashi gaban kotu ba sai ranar Talata.

Ta ce tana zarginsa da hada bidiyon na bogi, wanda hakan ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng