Buhari ya tura wakilai wurin bikin ɗan Gwamna Tambuwal

Buhari ya tura wakilai wurin bikin ɗan Gwamna Tambuwal

- Shugaba Buhari ya tura ministan yan sanda da wasu manyan jami'ai don su wakilce shi a wajen bikin dan Gwamna Tambuwal

- Najib dan Gwamna Tambuwal na Jihar Sokoto ya auri Amina Tafida yar Sanata Umar Tafida

- Shugaban kasar ya shawarci ma'auratan da su zauna lafiya su kuma girmama juna

Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa gayyatar auren Najib Aminu Waziri, dan gidan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ranar Asabar 15 ga watan Nuwamban shekarar 2020.

Najib ya auri Amina Umar Tafida, yar gidan Sanata Umar Tafida, Tafidan Argungu, a wani shagali da akayi a Argungu, Jihar Kebbi kamar yadda Daily Trust ya ruwaito.

Buhari ya tura wakilci bikin dan Tambuwal
Buhari ya tura wakilci bikin dan Tambuwal. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

Shugaba Buhari ya samu wakilcin ministan harkokin yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, Ministan Shari'a Abubakar Malami da babban mai taimaka masa bangaren yada labarai Malam Garba Shehu, da Musa Haro ma'aikacin fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa, a jawabin da ya yi ta bakin mai kakakinsa Malam Garba Shehu, ya shawarci ma'auratan da su ji tsoron Allah su girmama juna.

KU KARANTA: Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

"Ina shawartarku da ku zauna lafiya, kada ku gaji da juna," a cewar sa.

Shugaban ya kuma taya gwamnan Sokoto murnar shagalin kuma ya yi fatan a kare taron lafiya.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.

"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel