Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

- Wasu mazauna jihar Kaduna sun soki matakin gwamnatin jihar na ɓullo da harajin cigaba da kowanne baligi zai rika biya duk shekara

- Gwamnatin jihar ta ce harajin gudummawar ƴan jihar ne don aikin gine-gine da inganta jihar

- Wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu sunce bai dace a saka harajin ba yanzu duba da rashin ayyukan yi da talauci da wasu ƴan jihar ke ciki

Wasu mazauna Jihar Kaduna, a ranar Alhamis sun soki saka harajin cigaba na N1,000 da gwamnatin Kaduna ta saka a kan kowanne baligi duk shekara.

Hakan na cikin sashi na 9 (2) na dokar haraji na Jihar Kaduna ta shekarar 2020 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta hannun Hukumar Tattara Haraji na Jihar, KADIRS, a ranar Laraba ta ce zata fara aiki da dokar a shekarar 2021.

Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta saka
Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta saka. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar ya ce wannan harajin zai zama gudunmawar al'ummar jihar ne wurin yin gine-gine da sauya jihar.

Sai dai wasu mazauna jihar sun soki matakin da suka ce zai zama ƙarin nauyi a kan al'umma da a yanzu suke fama da wahalhalun rayuwa.

DUBA WANNAN: Gwamnan Jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu dokoki huɗu masu muhimmanci

Mercy Igabi, wata mai sayar da abinci a jihar yayin nuna rashin jin daɗinta game da dokar ta ce: "Wannan babban matsala ne ga masu ƙaramin ƙarfi. Kuma akwai waɗanda basu da aikin yi, samun abincin da za su ci ma aiki ne a yanzu."

Ibrahim Hussain, ma'aikacin gwamnati ya ce rashin adalci ne gwamnati ta ɗora wa harajin abin hawa, harajin hayan fili, harajin mai biyan kuɗi yanzu kuma ta nemi harajin cigaban jiha, inda ya ce harajin ya yi wa al'ummar jihar yawa.

"Ka samar wa matasa aikin yi kafin ka fara neman su biya haraji ga gwamnati," in ji Kayode James, wani makanike da ke kusa da Mogadishu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

"Muna da matasa da dama da ke yawo a tituna, ina ka ke tsammanin za su samo kuɗin da za su biya harajin? Wannan ba dai-dai bane musamman a lokacin da sana'o'i ke rushewa," in ji shi.

A wani labarin, gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.

Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel