FG za ta ciwo bashin dala miliyan 750 daga Bankin Duniya don talakawa a jihohi

FG za ta ciwo bashin dala miliyan 750 daga Bankin Duniya don talakawa a jihohi

- Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirye shiryen ciwo bashi don tallafawa wasu jihohin kasar

- Ministar kudi ta ce dole gwamnati ta dauki mataki kan musabbabin tashin kayyakin masarufi

- Za a shiga mawuyacin hali matukar gwamnati ta gaza shawo kan tsadar rayuwar da ake fama da ita

Gwamnatin tarayya tace tana shiryen shiryen ciwo bashin Dala miliyan 750 daga bankin duniya don farfado da tattalin arzikin wasu jihohi a Najeriya kamar yadda LIB ta ruwaito.

Ministar kudi, kasafi da tsare tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wajen bikin kaddamar da kwamitin farfado da tattalin arziki bayan barnar annobar korona (N-CARES) a Abuja ranar Juma'a, 13 ga Nuwamba.

Gwamnatin tarayya zata ciwo bashi Dala miliyan 750 daga bankin duniya
Gwamnatin tarayya zata ciwo bashi Dala miliyan 750 daga bankin duniya. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi

A cewar ministar, gwamnatin Najeriya "tana kokarin ciwo bashin dala miliyan 750 a madadin jihohin, don farfado da tattalin arzikinsu da kuma tallafawa marasa karfi."

Dangane da tsadar rayuwa da kuma tasirin COVID-19 a Najeriya, ministar tace, za a garari matukar gwamnati tayi bata dauki mataki akan hauhawar farashi a Najeriya ba.

"Abun ba zai yi dadi ba idan bamu dauki mataki akan tsadar rayuwar da muke fama da ita a Kasar nan. Dole mu tabbatar matakin da zamu dauma bayan COVID-19 ba zai cutar da yan Najeriya da kuma tattalin arziki ba," a cewarta.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari ta waya sun tattauna

A wani labarin, wasu mazauna Jihar Kaduna, a ranar Alhamis sun soki saka harajin cigaba na N1,000 da gwamnatin Kaduna ta saka a kan kowanne baligi duk shekara.

Hakan na cikin sashi na 9 (2) na dokar haraji na Jihar Kaduna ta shekarar 2020 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta hannun Hukumar Tattara Haraji na Jihar, KADIRS, a ranar Laraba ta ce zata fara aiki da dokar a shekarar 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel