Matashin da ya yi takarar shugaban kasa a 2019 ya yi zargin cewa FG na neman rayuwarsa

Matashin da ya yi takarar shugaban kasa a 2019 ya yi zargin cewa FG na neman rayuwarsa

- Dan takarar shugaban a karkashin inuwar jam'iyyar AAC a zaben 2019, Omoyele Sowere, ya zargi gwamnati da farautar rayuwarsa saboda zanga-zangar ENDSARS

- Matashin dan takarar ya yi zargin cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da wasu kusoshin gwamnati na da hannu a cikin lamarin

- A cewar matashin, babu wani da zai hana shi cigaba da gwagwarmayar neman 'yanci

Dan gwagwarmaya Kuma mawallafin jaridar SaharaReporters, Omoyele Sowere, ya zargi gwamnatin da kitsa kashe shi ko kuma kama shi saboda zanga-zangar ENDSARS.

Sowore, matashin da ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar AAC, ya bayyana hakan a jerin wasu takaitattun sakonni da ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Jami'an tsaron farin Kaya, DSS, sun taba kama Sowore a watan Agusta na shekarar 2019 a lokacin da ya jagoranci zanga-zangar juyin juya hali bayan faduwarsa a zaben shugaban kasa.

Matashin da ya yi takarar shugaban kasa a 2019 ya yi zargin cewa FG na neman rayuwarsa
Sowere a kotu
Asali: UGC

A cikin sakonni da ya wallafa, Sowore ya zargi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da wasu sauran kusoshin gwamnati da kitsa kama shi ko kuma kashe shi.

"Labarin da nake samu daga sashen sirri na rundunar soji (DIA) ya nuna cewa an saka gasa a kaina, a kan a kamani ko a kasheni a cikin sa'a 24 masu zuwa! Na samu wannan bayani ne daga hedikwatar tsaro da ke nan Abuja! Ina son kowa ya sani cewa hakan ba zai hanani cigaba da gwagwarmayar neman 'yanci da nake yi ba," kamar yadda Sowore ya wallafa.

A wani labarin daban da Legit.ng Hausa ta wallafa, wani malami ɗan shekara ashirin da tara ya shaidawa jami'an ƴan sanda cewa shaiɗan ne ya tunzura shi har ta kai jallin ya ƙwamushe ɗalibarsa ƴar shekara takwas a jihar Ogun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng