Dan dagacin kauye ya mutu bayan arangamar jami'an kwastam da 'yan sumogal
- Rikici ya barke a jihar Kebbi, tsakanin matasa masu sumogal da jami'an hukumar Kwastam
- Sakamakon rikicin, dan dagacin kauyen Budi mai suna Abdul-Rahman, ya rasa ransa
- Ya rasu ne sakamakon harbin da wani jami'in kwastam yayi masa a kafadarsa ta hagu
Dan dagacin wani kauye ya rasa ransa sakamakon rikicin jami'an kwastam da wasu matasa 'yan sumogal a jihar Kebbi., jaridar The Punch ta wallafa.
Rikicin ya hargitse tsakanin jami'an kwastam na Kaduna da suke aiki a jihar Kebbi, da wasu matasa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi.
Kamar yadda rahotonni suka kammala, wanda aka kashe, Abdul-Rahman Sani, da ne ga dagacin kauyen Budi, Alhaji Sani Muhammad, na karamar hukumar Bunza.
Tsohon sakataren kungiyar bunkasa karamar hukumar Bunza, Alhaji Sahabi Chindo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, "Jami'an kwastam sun tare wasu ababen hawan matasan garin Bunza.
"Matasan sun tsaya suna ciniki da jami'an, bayan sun gama, sai matasan suka je daukar ababen hawansu, kawai sai rikici ya hada jami'an da marigayin.
"Jami'an sun dakatar da Abdul-Rahman, inda suka ce in dai ya matsa kusa da su za su harbeshi, yana matsawa suka harbeshi."
Kakakin hukumar kwastam na Zone B, na Kaduna, ASP Mailafiya Magaji, yace, "Yayin da jami'ansu suna sintiri wuraren layin Kamba kusa da Bunza, sai suka ci karo da wani abin hawa cike da shinkafa 'yar kasar waje, wacce nake kyautata zaton sumogal din ta aka yi."
A cewar Magaji, "Bayan jami'an sun ci karo da matasan, kawai sai ga wasu matasan daban, dauke da makamai. Hakan ya janyo rikici tsakaninsu.
"Matasan sun yi yunkurin kai wa jami'an farmaki, sai suka yi harbi, inda alburushin ya sami daya daga cikin matasan a kafadarsa ta hagu, take a nan aka kai shi asibiti.
"Duk da dai wasu daga cikin jami'an sun samu raunuka, amma matashin ya rasa ransa babu dadewa da kai shi asibiti."
KU KARANTA: Gwamna Inuwa ya kai wa wanda ya taka zuwa Abuja wurin Buhari dauki bayan ya koka da ciwon kafa
KU KARANTA: Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara
A wani labari na daban, Murtala Gwarmai, mai ba wa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin matasa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya rarraba wa matasa jakuna a ranar Alhamis.
Gwarmai, ya gwangwaje matasan da jakuna, babura da kekunan hawa da sauran su, Daily Trust ta wallafa. Kamar yadda rahotonni suka kammala, matasa a kalla 40 ne suka sha daga romon damokaradiyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng