Romon damokaradiyya: Hadimin Ganduje ya gwangwaje jama'a da tattalin Jakuna

Romon damokaradiyya: Hadimin Ganduje ya gwangwaje jama'a da tattalin Jakuna

- Mai ba wa gwamna Ganduje shawara a harkokin matasa, Murtala Gwarmai, ya gwangwaje matasan jihar Kano da kyautar jakuna

- Matasan guda 40 da suka amfana da kyautar sun nuna farin cikinsu a fili, har da yi masa addu'o'in samun nasara a rayuwarsa

- Kamar yadda bayanai suka kammala, matasan da kansu suka bukaci ya raba musu jakai, babura da kekuna don inganta sana'o'insu

Murtala Gwarmai, mai ba wa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin matasa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya rarraba wa matasa jakuna a ranar Alhamis.

Gwarmai, ya gwangwaje matasan da jakuna, babura da kekunan hawa da sauran su, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda rahotonni suka kammala, matasa a kalla 40 ne suka sha daga romon damokaradiyyar.

A cewar hadimin, matasan sun bukaci ya basu tallafin jakuna don su inganta sana'arsu, saboda su ji dadin safarar kayan gini, kamar yashi da duwatsu.

Matasan sun bayyana farincikinsu a fili, suna gode masa da yi masa addu'ar samun nasara a harkokin da yasa gaba.

KU KARANTA: Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki

Romon damokaradiyya: Hadimin Ganduje ya gwangwaje jama'a da tattalin Jakuna
Romon damokaradiyya: Hadimin Ganduje ya gwangwaje jama'a da tattalin Jakuna. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana barnar da tayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasafi da kididdiga na gidan gwamnatin jihar Kwara, Isiaka Kareem, ya sanar da babbar kotun tarayya da ke Legas cewa mai gidansa ya umarcesu da su ba wata Abdul Adama, wacce ta taba zama hadimar tsohon gwamnan Kwara, Dr Bukola Saraki, Naira miliyan 100 a cikin kudin amfanin gidan gwamnatin jihar.

A cewarsa, ana biyan Adama albashi kowanne wata tsakanin 2003 zuwa 2011, lokacin da Saraki yana kan mulkin jihar.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya gabatar musu da Adama a matsayin hadimarsa ta musamman, sannan duk wata sai an biya Adama a bisa umarnin Saraki, da sunan "kudin tsaro da na ko-ta-kwana".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel