Gwamna Inuwa ya kai wa wanda ya taka zuwa Abuja wurin Buhari dauki bayan ya koka da ciwon kafa
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya taimaka wa Dahiru Buba, wanda yayi tattaki zuwa Abuja lokacin da Buhari ya ci zabe
- Idan ba a manta ba, Buba yayi tattaki tun daga Gombe, zuwa Abuja don nuna kauna ga shugaba Buhari
- Bayan tattakin ne ciwon kafa ya kama shi, har yayi ta neman taimakon gwamnati da al'umma don neman na magani
Gwamna Inuwa Yahaya, ya taimaka wa mutumin da ciwon kafa ya kama shi bayan ya yi tattaki tun daga Jihar Gombe zuwa Abuja don murnar nasarar Buhari a 2019.
Gwamnan ya taimaki Dahiru Buba, dan asalin karamar hukumar Dukku, wanda yake fama da ciwon kafa, bayan tattakin da yayi a watan Fabrairun 2019 don taya Buhari murnar kara zabensa da aka yi a karo na biyu.
Buba ya dade yana rokon al'umma da su taimaka masa saboda ciwon kafar da yake fama da shi.
Bayan hakan ne wata takarda, wacce Ismaila Uba Misilli, hadimin gwamnan na musamman ya saki a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, wacce take bayyana yadda gwamnatin ta mayar da mutumin asibitin gidan gwamnati, aka kai shi bangaren kula da lafiya na musamman.
Kamar yadda takardar ta zo: "A bisa umarnin gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, an kai Dahiru Buba asibitin gidan gwamnatin jihar Gombe, inda za a mayar da shi bangare na musamman don kula da lafiyarsa."
KU KARANTA: Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki
KU KARANTA: Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara
A wani labari na daban, wani saurayi ya wallafa yadda zuciyarsa ta sosu a kan wani kalubale da ya fuskanta a soyayya. Saurayin mai suna Skinnyniggr ya wallafa hotunan yadda ta kaya tsakaninsa da buduwarsa wacce yake mutukar kauna.
Budurwarsa ta tura masa sako, inda ta ke sanar da shi cewa saura kwanaki kadan a daura mata aure . Wani Chimuanyarhs ya yi tsokaci a karkashin wallafar, inda yace shi ma ya fuskanci kalubale a soyayya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng