Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara
- Tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki, yana umartar a kwashi naira miliyan 100 duk wata a ba wa Adama, lokacin yana kan mulki, cewar Kareem
- Isiaka Kareem, sakataran Saraki, a lokacin ya na gwamnan jihar, ya shaida wa babbar kotu haka, yayin da aka kirashi bayar da shaida a gaban babbar kotun Legas
- Dama EFCC tana binciken Saraki a kan kwasar naira biliyan 12 daga asusun gwamnatin jihar, kuma ya dura wasu kudaden a cikin asusunsa na wasu bankuna
Tsohon shugaban kasafi da kididdiga na gidan gwamnatin jihar Kwara, Isiaka Kareem, ya sanar da babbar kotun tarayya da ke Legas cewa mai gidansa ya umarcesu da su ba wata Abdul Adama, wacce ta taba zama hadimar tsohon gwamnan Kwara, Dr Bukola Saraki, Naira miliyan 100 a cikin kudin amfanin gidan gwamnatin jihar.
A cewarsa, ana biyan Adama albashi kowanne wata tsakanin 2003 zuwa 2011, lokacin da Saraki yana kan mulkin jihar.
A cewarsa, tsohon gwamnan ya gabatar musu da Adama a matsayin hadimarsa ta musamman, sannan duk wata sai an biya Adama a bisa umarnin Saraki, da sunan "kudin tsaro da na ko-ta-kwana".
Kareem ya bayyana a gaban kotu ranar Laraba yayin da EFCC suka bukaci tsohon sakataren Saraki ya bayar da shaida, The Punch ta wallafa.
Dama mai shari'a Mohammed Liman ya umarci a binciki gida mai lamba 17A a layin McDonald da ke Ikoyi. Saboda EFCC ta zargi wasu ayyuka na rashin gaskiya suna faruwa a gidan.
EFCC ta zargi Saraki, wanda ya rike kujerar gwamnan Kwara tsakanin 2003 da 2011, da kwasar naira biliyan 12 daga cikin asusun gwamnatin jihar, inda ya tura wasu kudaden a asusunsa na wasu bankuna ta wata hadimarsa ta musamman, Abdul Adama, a lokuta daban-daban.
KU KARANTA: An tsinci gawar budurwa mai shekaru 22 cikin kwata a jihar Anambra
KU KARANTA: Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki
A wani labari na daban, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo ya kwatanta kansa a matsayin sabuwar ma'anar demokradiyya, The Cable ta wallafa.
Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ake rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu, wanda aka yi a Samuel Ogbemudia a Benin, babban birnin jihar Edo. An yi taron rantsarwar gwamnan da ta mataimakinsa, Philip Shaibu.
A cewar Obaseki, lokaci ya yi da za a kawar da banbance-banbancen siyasa kuma a tabbatar ya ba kowa hakkinsa don taimakon mutanen jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng