Mummuna, kazami kuma talakan namiji yana bata min rai - Jarumar fim

Mummuna, kazami kuma talakan namiji yana bata min rai - Jarumar fim

- Wata jarumar fim, mai suna Sandra Alhassan, ta bayyana irin matakin da saurayi zai kai, in dai yana so tayi soyayya da shi

- Kyakkyawar jarumar ta ce sai namiji yana da kyau, tsafta da kudi tukunna zata iya sauraronsa

- A cewarta, ran ta yana matukar baci idan kazami, gaja, talaka kuma mummuna ya tunkarota da soyayya

Jarumar finafinan Yarabawa, Sandra Alhassan, ta bayyana irin saurayin da zata iya kulawa, da wanda ko kallo bai isheta ba, jaridar Vanguard ta wallafa.

Jarumar, wacce mahaifiyarta asalin 'yar jihar Edo ce, mahaifinta kuma dan jihar Kano, ta ce ta ki jinin kazamin saurayi.

Kyakkyawar, dirarriyar jarumar ta ce tana matukar son kula samari masu kyau, tsafta, aji da kuma dukiya. Yayin da ta tsani munana, talakawa da kuma kazaman samari.

Kamar yadda ta wallafa: "Ba zan iya sauraron kazamai, gajoji da kuma talakawan samari ba. Sannan na tsani ganin saurayi mai cike da yarinta.

"Duk da ana cewa, so hana ganin laifi, amma gaskiya ina da matukar zaben samari. Idan kuwa aka zo batun aure, kankat kenan. Muna ganin yadda ake samun matsaloli a aure; wasu har kashe junansu suke yi.

"Ina shawartar 'yan uwana mata da su kiyaye fada wa aure ba tare da sun tantance maza ba. A kula da yanayin miji kafin a kai ga yin aure. Idan mutum yayi aure, ana sa ran har karshen rayuwarsa kenan."

A cewarta, ta rabu da saurayinta wanda ta fi so fiye da kowa saboda ta shiga harkar fim, amma mahaifiyarta ta bata kwarin guiwa. Tayi kuka matuka, amma bayan ta shiga fim, sai ta kwantar da hankali.

KU KARANTA: Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara

Mummuna, kazami kuma talakan namiji yana bata min rai - Jarumar fim
Mummuna, kazami kuma talakan namiji yana bata min rai - Jarumar fim. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Miji ya maka matarsa a kotu a kan shigar banza da take

A wani labari na daban, Gwamna Inuwa Yahaya, ya taimaka wa mutumin da ciwon kafa ya kama shi bayan ya yi tattaki tun daga Jihar Gombe zuwa Abuja don murnar nasarar Buhari a 2019.

Gwamnan ya taimaki Dahiru Buba, dan asalin karamar hukumar Dukku, wanda yake fama da ciwon kafa, bayan tattakin da yayi a watan Fabrairun 2019 don taya Buhari murnar kara zabensa da aka yi a karo na biyu.

Buba ya dade yana rokon al'umma da su taimaka masa saboda ciwon kafar da yake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng