Yanzu-yanzu: Shahrarren dan kwallon , Mohamed Salah, ya kamu da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Shahrarren dan kwallon , Mohamed Salah, ya kamu da cutar Coronavirus

Shahrarren dan kwallon kasar Masar kuma mai bugawa kungiyar kwallon Liverpool, Mohamed Salah ya kamu da muguwar cutar Coronavirus.

Kungiyar kwallon kasar Masar ce ta sanar da hakan a shafinta na yanar gizo ranar Juma'a, Punch ta gano.

Ya kamu da cutar ne yayinda ya tafi wasa kuma zai killace kansa.

"Gwajin cutar Koronan da muka gudanar kan yan kwallonmu ya nuna cewa dan wasa, Mohamed Salah, tauraron Liverpool, ya kamu da cutar," jawabin yace.

"Babu wasu alamun kamuwa da cutar tattare da shi, kuma sauran yan kwallon basu kamu ba."

Yanzu-yanzu: Shahrarren dan kwallon , Mohamed Salah, ya kamu da cutar Coronavirus
Yanzu-yanzu: Shahrarren dan kwallon , Mohamed Salah, ya kamu da cutar Coronavirus Credit: @MoSalah
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel