Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'

Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'

- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, mutum ne da ya yi kaurin suna a duniya wajen rudani da rikita-rikita

- Jagoran mabiya addinin Kirista na duniya, Fafaroma Francis, ya ce shugaba Trump ba Kirista bane

- A cewar Fafaroma Francis, duk wani mutum da zai yi tunanin gina katanga, ba gina gada ba, wannan mutum ba Kirista bane

Fafaroma Francis, jagoran mabiya addinin Kirista a duniya, ya ce shugaban kasar Amurka, "Donald Trump ba kirista bane."

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke mayar da martani a kan alkawarin da Trump ya dauka cewa zai kori bakin 'yan gudun hijira daga Amurka tare da tilasta kasar Mexico biyan kudin gina Katanga a iyakarta da Amurka.

"Duk wani mutum da ke tunanin gina katanga, ba gina gada ba, ba kirista bane," kamar yadda Fafaroma ya fada yayin amsa tambayar dan jarida a birnin Rome na kasar Italy bayan dawowarsa daga wata ziyara ta kwana 6 a kasar Mexico.

KARANTA: Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

"Ba zan shiga batun siyasa ba," Fafaroma ya fada a matsayin amsar tambayar ko zai shawarci mabiya Cocin Katolika a kan dan takarar da ya kamata su zaba a kasar Amurka.

Fafaroma Francis ya cigaba da cewa; "abinda na fada shine cewa Shi (Trump) ba Kirista bane matukar ya furta hakan."

Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'
Fafaroma Francis
Asali: UGC

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa an sallami shugaban kasar Amurka, Donald Trump daga asibitin Sojojin Walter Reed dake Bethesda inda yake jinya bayan kasuwa da cutar Coronavirus.

KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari

Shugaban kasan da kansa ya bayyana hakan da yammacin Litinin a shafinsa na Tuwita.

Trump ya jaddada cewa ko kadan bai tsoron cutar Korona kuma ya yi kira ga mutane su daina tsoron cutar saboda ba komai bace.

"Zan bar asibitin Walter Reed yau daidai karfe 6:30 na yamma. Ina samun sauki. Ku daina tsoron COVID. Kada ku bari tayi tasiri a rayuwarku. Na fi jin dadi yanzu fiye da shekaru 20 baya," a cewarsa.

Likitan Donald Trump, Dr Sean Conley, ya ce shugaban kasan zai koma fadar White House duk da cewa "ba wai ya gama samun lafiya ba" kuma zai cigaba da shan manyan magunguna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel