Gwamnan Jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu dokoki huɗu masu muhimmanci
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu dokoki hudu masu muhimmanci
- Dokokin sun shafi samar da sana'o'i, samar da ruwan sha a kauyuka, zakka, kaddamar da sabon tambarin jihar
- Gwamnan ya ce sabbin dokokin za su taimaka wurin sauya jihar ta Zamfara ta zama birnin da kowa zai yi alfahari da ita
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya rattaba hannu a kan wasu kudirin dokoki guda hudu a jiharsa kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Dokokin sun hada da dokar kirkirar sabon tambarin gwamnatin Jihar da kuma dokar kafa hukumar koyar da sana'o'i.
DUBA WANNAN: 2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi
Sauran sun hada dokar yi wa hukumar zakka ta 2013 garambawul da suka hada karbar zakka, raba ta da kuma dokar kafa hukumar samar da ruwa a karkara da wasu harkoki masu alaka da shi.
Dokar kafa tambarin na gwamnati ya tanadi yadda za ayi amfani da shi da kuma hukuncin da za a yi wa wanda aka samu yana amfani da shi ba ta hanyar data dace ba. Dole duk wani aiki ko kwangila na gwamnati ya kasance yana dauke da tambarin.
Garambawul din da aka yi wa dokar zakar ya canja ma'aikatan hukumar daga na wucin gadi zuwa ma'aikatan dindindin da aka fiddo daga masarautu 17 na jihar.
KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi
Dokar da aka kafa na samar da ruwan fanfo ga kauyuka zai kula da tabbatar da samar da tsaftacacen ruwa ga kauyuka da karkara.
Dokar ta hudu na koyar da sana'a za ta rika horas da tallafawa matasa samun aikin yi bisa tsarin gwamnati na samar wa dimbin matasan jihar ayyukan yi.
Da ya ke rattaba hannu kan kudirin domin su zama dokoki, Gwamna Mohammed ya ce gwamnatinsa za ta samar da tsare-tsare da za su gina sabuwar Jihar Zamfara da kowa zai yi alfahari da ita.
A wani labarin, abokan wani attajirin Zimbabwe, Genius Kadungare wanda yafi shahara da Ginimbi a fagen zamantakewa sunce za a binne shi ne da tarin daloli, wata majiya ta kusa ta ruwaito.
Dan kasuwar wanda ya yi rayuwa ta alfarma, shine ya bar wasiyar, a cewar jaridar Herald.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng