'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Masu garkuwa sun tare matafiya a kusa da garin Rijana a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Sun harbe mutum guda har lahira sun kuma yi awon gaba da matafiya masu yawa

- Wani mazaunin kauyen Rijana, Ahmed Iliyasu ya tabbatar da afkuwar lamarin da ya ce ya faru da safe

'Yan bindiga a jiya (Laraba) sun kashe matafiyi guda daya kuma sun yi garkuwa da wasu da dama a kusa da garin Rijana da ke babban titin Kaduna zuwa Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin Rijana, Ahmed Iliyasu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8.00 na safe a Gadar Malam Mamman da ke nisan kilomita kadan daga garin Rijana.

An kashe mutum ɗaya, an sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja
An kashe mutum ɗaya, an sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun tafi har gidansa sun sace hakimi a jihar Zamfara

Ya ce 'yan bindigan sun tare titin kafin suka tafka barnarsu. Ya ce sun harbe matafiyi guda daya har lahira sannan suka yi garkuwa da sauran.

Daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin, Arch. Mudassur Ladan ya ce yana tuki a mota zuwa Abuja ne a lokacin da maharan suka bullo daga daji suka fara harbe-harben bindiga ba kakkautawa.

KU KARANTA: Mijina ya yi min ƙaryar nice matarsa ta biyu, alhalin nice ta shida - Mata ta shaidawa kotu

"Maharan guda hudu suna ta harbi babu kakkautawa. Na ga motocci guda hudu sun tsaya a gefen titi yayin da mutanen da ke cikin motoccin suke kwance a kasa.

"Mutum biyu sun biyo ta baya na suka fara harbi. Na afka cikin daji da motar amma daga bisani dole muka fita muka bar motar.

"Daga bisani mun dawo wurin. Mun tarar da 'yan sanda kuma mun ga mutum daya ya mutu sannan wasu da raunikan bindiga," kamar yadda ya fadi.

Da aka tuntube kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya bukaci a bashi lokaci ya tabbatar da rahoton daga kwamandan yankin amma bai bada bayani ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya naɗa gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle "Shettiman Sakkwato".

A cikin wasikar da ke ɗauke da sanarwar zuwa ga Gwamna Matawalle, mai ɗauke da sa hannun Sarkin Musulmi, Sultan ya ce ya naɗa masa sarautar ne don mutunci da girmamama masarautun gargajiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel