Yanzu-yanzu: An tsige kakakin majalisar Jihar Imo

Yanzu-yanzu: An tsige kakakin majalisar Jihar Imo

- Mista Chiji Collins ya rasa muƙaminsa na kakakin majalisar jihar Imo kan zarginsa da aikata wasu laifuka masu alaka da bannatar da kudi da amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba

- Ƴan majalisa 19 cikin 27 ne suka goyi bayan tsige Collins a yayin zaman majalisar ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamban Shekarar 2020

- Bayan tsige Collins, Majalisar ta zaɓi Mista Paul Emeziem mai wakiltar Onuimo ya zama sabon kakakin majalisar

An tsige Kakakin Majalisar Jihar Imo, Mista Chiji Collins kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

An tsige Collins ne yayin zaman majalisar a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba a ginin majalisar da ke Owerri, babban birnin jihar.

Yanzu-yanzu: An tsige kakakin majalisar Jihar Imo
Yanzu-yanzu: An tsige kakakin majalisar Jihar Imo. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnan Jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu dokoki huɗu masu muhimmanci

A lokacin da aka gabatar da kuɗirin tsige kakakin majalisar, ƴan majalisa guda 19 cikin 27 sun goyi bayan tsigewar.

An tsige Mista Collins ne kan zargin kashe kuɗade ba bisa ka'ida ba, saba dokokin majalisa, babakere da wasu laifukan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Bayan tsige shi, ƴan majalisar sun zaɓi Mista Paul Emeziem daga ƙaramar hukumar Onuimo a matsayin sabon kakakin majalisar.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu mazauna Jihar Kaduna, a ranar Alhamis sun soki saka harajin cigaba na N1,000 da gwamnatin Kaduna ta saka a kan kowanne baligi duk shekara.

Hakan na cikin sashi na 9 (2) na dokar haraji na Jihar Kaduna ta shekarar 2020 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta hannun Hukumar Tattara Haraji na Jihar, KADIRS, a ranar Laraba ta ce zata fara aiki da dokar a shekarar 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164