Zamu fara bibiyan fina-finan Hausa a Youtube, Hukumar tace fim a Kano

Zamu fara bibiyan fina-finan Hausa a Youtube, Hukumar tace fim a Kano

- Domin tabbatar da tsare tarbiyyar al'ummar Kano, hukumar tace fina-finai zata fara bibiyan yanar gizo

- Shugaba hukumar ya bukaci masu shafukan watsa fina-finan Hausa su garzayo ofishinsa domin tattaunawa

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta ce shirya take ta fara bibiyan tashoshin fina-finan Hausa a shafin Youtube domin kare al'ummar Kano daga fina-finan rashin tarbiyya.

Sakataren hukumar, Malam Isma'il Na'abba, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda yake hira da yan jarida a Kano.

"Ya zama wajibi mu tsaftace wajen, saboda masu fina-finai da dama sun samu hanyar watsa rashin tarbiyyarsu saboda ba'a bibiyansu."

"Bisa ga manufar kafa hukumar, muna gayyatan masu shafuka a Youtube inda ake daura bidiyoyin Hausa saboda mu fahimci juna," yace.

"Hukumar na da karfin tace abubuwa da bibiya ko da rubutu ne, bidiyo ne ko odiyo, da ake nufin watsawa mutane."

"Mun bayyana karara cewa wajibi ne kowa yanzu ya kawo fim dinsa ofishin hukumar domin tace ta kafin ya daura a shafinsa, " ya kara.

Na'abba wanda yayi gargadi yace hukumar zata ci taran duk wanda ya saba dokar.

KU KARANTA: Ku daina yafewa mayakan kungiyar Boko Haram, ku yi koyi da kasar UAE; Majalisa ga FG

Zamu fara bibiyan fina-finan Hausan a Youtube, Hukumar tace fim a Kano
Zamu fara bibiyan fina-finan Hausan a Youtube, Hukumar tace fim a Kano Credit: @Premiumtimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku daina yafewa mayakan kungiyar Boko Haram, ku yi koyi da kasar UAE; Majalisa ga FG

A wani labarin daban, jarumi a masana'antar Kannywood, Ibrahim Maishinku, ya bayyana yadda ya tsallaka rijiya da baya yayinda yan bindiga masu garkuwa da mutane suka bude musu wuta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A jawabin da ya daura a shafinsa na Instagram, Maishinku ya bayyana cewa hakan ya faru da su da yammacin Talata bayan Sallar Magariba.

A cewarsa, yan bindiga sun kwashe kimanin mituna talatin suna bude musu wuta kuna sun yi awon gaba da abokinsa suna neman kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel