Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG

Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG

- Gwamnatin tarayya ta ce kamata ya yi ace ana sayar da litar man fetur akan N181 maimakon N161 da ake sayar da ita yanzu

- Ministan man fetur Timipre Silver, ya bayyana cewa FG ta yi asarar N10.413trn daga 2006 zuwa 2019 da kuma N2.193trn tsakanin 2016 zuwa 2019

- La'akari da karyewar tattalin arziki, da kuma kudaden da ake kashewa wajen shigon da man, Silver ya ce, ya zama dole a janye tallafin man fetur din

Kamata ya yi ace ana sayar da litar man fetur akan N181, idan har za a yi la'akari da kudaden da ake kashewa wajen sarrafashi, mai makon N161 da ake sayar da shi yanzu, cewar FG.

Ministan cikin gida kan man fetur, Timipre Silver, ya bayyana hakan yana mai nuni da cewa Nigeria ta yi asarar N10.413trn daga 2006 zuwa 2019, a tallafin man fetur din.

A tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019 kuwa, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta batar da N2.193trn, duk don ganin ta bayar da tallafin man fetur din.

KARANTA WANNAN: Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a kasar Ghana

Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG
Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG
Source: Twitter

Silver ya yi jawabi ne a wani taro tsakanin Gwmanatin tarayya da kungiyar kwadago, a dakin taron fadar shugaban kasa, Abuja, a ranar Talata.

Gwamnatin tarayya na karkashin wakilcin ministan kwadago, Dr Chris Ngige da ministoci biyar hadi da shuwagabannin hukumomi; yayin da Ayuba Wabba da Quadri Olaleye suka wakilci kungiyoyin kwadago na NLC da TUC.

A cewar Silver, an kai wata makura a bangaren ma'aikatar man fetur, uwa uba yadda farashin dala ya ki dai dai tuwa da kudin Nigeria, wanda ya kamata fetur din ya zamo N181.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili

Ministan ya ce la'akari da karin kudin fetur din yanzu, har yanzu shine farashi mafi sauki a kasashen Yammacin Afrika.

A kasar Senegal ana sayar da lita N549, Cameroon akan N449 Benin akan N359, Ghana akan N332 da kuma sauran kasashen da ke makwaftaka da Nigeria.

Ya ce: "Tsakanin 2016 zuwa 2019, muna asarar akalla N1bn a kowacce rana saboda lalitarmu kamar kwando ce a lokacin. Kafin ma lokacin, har N3.7bn muna asara kowacce rana.

"To mai makon biyan tallafin man fetur, gwanda mu dinke barakarmu ta wannan fannin, ko ba komai zamu samu riba mai yawa, dole a janye tallafin man, don ci gaban kasar.

"Amma duk da cewa mun kara farashin man, halin da ake ciki yanzu, farashin mai yana N161 a kowacce lita, kamata ya yi a sayar da lita kan N181, kasarmu ce mai saukin farashin fetur."

A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa karin farashin man fetur da wutar lantarki a wannan lokacin zai kara jefa 'yan Nigeria cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta janye karin, yana mai cewa kamata ya yi shugaban ya dinke barakar da ake samu a gwamnatinsa maimakon karin farashin man fetur da lantarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel