El-Rufai ya yi ƙarar tsohon hadimin Goodluck Jonathan da wasu mutum 6 a kotu

El-Rufai ya yi ƙarar tsohon hadimin Goodluck Jonathan da wasu mutum 6 a kotu

- Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi karar Reno Omokri tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu mutane 6

- Gwamnan yana zarginsu da wallafa labaran da ya ce na karya ne game da shi wadda hakan ya bata masa suna tare da taba masa mutunci

- Baya ga bukatar su wallafa wasikun neman afuwa a wurinsa, El-Rufai ya bukaci su biya shi jimilar kudi Naira biliyan 1.5 kuma

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi karar Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, Mai kare hakkin bil-adama, Farfesa Chidi Odinkalu da wasu masu kare hakkin bil-adama 5.

Gwamna El-Rufai na neman su biya shi tarar Naira biliyan 1.5 don zarginsu da bata masa suna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi karar hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan da wasu
El-Rufai ya yi karar hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan da wasu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli

A cikin kararrakin mabanbanta da lauyansa A.U. Mustapha (SAN) ya shigar a babban kotun Abuja, El-Rufai ya kuma yi karar jaridar ThisDay, Daniel Elombah, Elombah Communications, Barista Joseph Onu da Auta Nyada.

A karar da ya shigar kan Omokri, El-Rufai ya ce kalaman da aka jingina masa a jaridar Thisday na ranar Lahadi 14 ga watan Yunin 2020 mai taken: 'Sakon imel na El-Rufai na cewa ana yi wa mata masu yi wa kasa hidima da suka fito daga kudu kallon karuwai' ya bata masa suna, ya kara da cewa 'karya ce mara tushe da aka yi don bata masa suna.'

Gwamnan ya bukaci a biya shi Naira miliyan 500 na bata masa suna sannan a nemi afuwarsa a wallafa a jaridar.

A karar da ya shigar kan Odinkalu, Daniel Elombah da Elombah Communications, El-Rufai ya ce wallafar da aka yi mai taken: 'Jerin sunayen masu suka 25 da suka sha wahala a hannun El-Rufai da Chidi Odinkalu ya rubuta' sannan aka wallafa a shafin Elombah.com a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 shima 'sharri aka yi masa, ya saba doka kuma babu wani hujja.'

KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

A wannan karar ita ma ya nemi a biya shi Naira miliyan 500 kuma a nemi afuwarsa kan 'rubutun da ya bata masa suna sosai.'

El-Rufai ya kuma ce wata wasika da Joseph Onu da Nyada suka rubuta a ranar 19 ga watan Agustan 2020 ga shugaban kungiyoyin lauyoyi ta Najeriya (NBA) ga shugaban kungiyar Farfesa Koyinsola Ajayi, SAN, da wasu na neman janye gayyatar da aka masa na hallartar taron kungiyar shima ya 'bata masa suna da taba mutuncinsa.'

Kazalika, El-Rufai ya bukaci a nemi afuwarsa a kuma biya shi Naira miliyan 500.

Kotu ba ta tsayar da ranar fara sauraron karar ba.

A wani labarin, wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu.

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel