Akawun kotu ya harbe alkali, ya sheka lahira a take

Akawun kotu ya harbe alkali, ya sheka lahira a take

- An harbe alkalin kotu a Philippines, a cikin harabar kotun da take alkalanci

- Kamar yadda bayanai suka bayyana, akawun kotun ne ya harbe alkalin

- Bayan ya harbeta, ya harbe kansa, har yanzu ba a tabbatar da dalilin ba

An harbe wata alkalin kotu a kasar Philippines, a cikin harabar kotun da take alkalanci a birnin Manilla.

Alkalin ta rasu bayan wani dan lokacin, sakamakon raunukan da ta samu saboda harbin.

Bayan 'yan sanda sun yi bincike, sun gano cewa akawun kotun, Amador Rebato, ne ya harbe alkalin mai suna Theresa Abadilla, daga bisani ya kashe kansa da kansa.

Har yanzu dai ba a samu wani bayani a kan dalilin da yasa akawun ya harbe alkalin ba.

Sai dai kafafen yada labarai na kasar, sun ruwaito yadda aka yi ta kashe masu shari'a da dama, inda Abadilla ce mutum ta 51 da aka kashe tun bayan hawa mulkin shugaba Rodrigo Duterte a 2016.

KU KARANTA: A gida na haifa 'ya'ya 13 ba tare da zuwa asibiti ba, mahaifiyar yara 15

Akawun kotu ya harbe alkali, ya sheka lahira a take
Akawun kotu ya harbe alkali, ya sheka lahira a take. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya bayyana mutuwar Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, a matsayin babbar asara ga Najeriya da demokradiyya.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, lokacin da yake mika sakon ta'aziyyarsa, Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda yace, "Mun samu wannan mummunan labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar Kaduna na farko a mulkin farar hula, Malam Abdulkadir Balarabe Musa, wanda ya rasu a lokacin da muka fi bukatarsa."

A cewarsa, "Marigayin ne da ire-irensa suka gyara jihar Kaduna. Mun karu kwarai da marigayin musamman a kan harkar siyasa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng