Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki

Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki

- Tun da na kashe aurena rayuwata take cikin hatsari, cewar gimbiya Aanu ta Oyo

- Ta ce da kyar ta tsere, sakamakon yunkurin yin garkuwa da ita da aka so yi

- A cewarta, matsawar wani abu ya faru da ita ko kuma yaranta, to Alaafin din Oyo za a kama

Rayuwata tana cikin hatsari saboda mutuwar aurena, cewar tsohuwar matar Alaafin din Oyo, gimbiya Aanu.

Auren Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da na daya daga cikin matansa, Gimbiya Aanu, ya na cikin tsaka mai wuya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

A wata wallafa da Gimbiya Aanu tayi a shafinta na kafar sada zumuntar zamani, ta sanar da tashin hankalin da take ciki, bayan ta yanke shawarar kashe aurenta.

Kamar yadda Aanu tace, ba za ta iya cigaba da zaman auren da yake cike da tashin hankali ba. Ta ce tun bayan barin fadar basaraken, ana kai wa rayuwarta hari. Tace yanzu haka an so a yi garkuwa da ita, amma ba a samu nasara ba.

Ta sanar da duniya cewa matsawar wani abu ya same ta ko kuma yaranta, to basaraken ne yake da alhakin yin hakan.

KU KARANTA: Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000

Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki
Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon budurwa tana ragargaza gilasan motar saurayi a kan cin amanarta da yayi

A wani labari na daban, Hussaina Salisu, 'yar karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, ta ce cikin yaranta 15, ta haifi guda 13 ita kadai a gida.

Ta ce bata taba fuskantar wasu wahalhalu ba yayin haihuwar yaranta ba. A cewarta, "cikin yarana 15, guda 2 ne kadai na haifa a asibiti."

Matar, mai shekaru 54 ta ce ba za ta shawarci wata mace ta yi kwatankwacin abinda tayi ba, inda tace "Da ban samu wayewa ba, da yanzu ban tsinci kaina a halin da na ke ba a yanzu."

A cewarta, lokacin da ta haifi yaronta na fari, tana da shekaru 14 a duniya, shekaru fiye da 28 da suka wuce kenan, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel