Budurwa ta bayyana barnar da tayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata
- Wata budurwa ta sanar da matakin da ta dauka bayan ta gano saurayinta zai auri wata daban
- Ta ce sai da ta tabbatar da kayan da zai sa ranar daurin auren, sai ta lalata su
- Ta yi amfani da almakashi ta yayyanka kayan, sannan tayi fatan ba zai gano ba sai ranar bikin
Wata mata ta bayar da labarin matakin da ta dauka bayan ta gane saurayinta zai auri wata daban.
Matar ta yi amfani da shafinta na Twitter inda ta fadi abinda ta yi wa saurayinta bayan jin za a daura masa aure da wata.
Ta sanar da labarin ne bayan OAP Toolz ya tambayi mutane a kan matakin da suka dauka bayan an yaudaresu.
Matar ta amsa da: "Bayan na gano cewa zai yi aure, na samu almakashi ba yayyanka kayan da zaisa a ranar auren, hakan ya faru jiya ne."
Ta kara da cewa, sai da ta yi fatan bai gane ta lalata rigar ba har sai yayi lattin siyan wata rigar, kenan ranar auren, yadda ba zai iya siyan wata ba.
KU KARANTA: Duba garejin dan wasan kwallo Obafemi Martins, mai dauke da kasaitattun motocin kece raini
KU KARANTA: Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari
A wani labari na daban, al'amarin 'yan bindiga kullum kara faskara yake yi a jihar Zamfara. Don yanzu haka sun fara sanya wa manoma haraji kafin su yi girbi.
Wani Abdussalam Ibrahim Ahmed ya ce: "Yan bindiga sun umarcemu da mu biya N800,000 matsawar muna son su bar mu mu yi noma cikin kwanciyar hankali, kuma har mun biya."
Kamar yadda yace, sai da suka biya haraji kafin su bar su su yi girbi. Har yanzu, 'yan ta'adda suna cigaba da kashe-kashe, kai hare-hare, har da yi wa mata fyade a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng