Sojoji sun kashe 'yan ta'adda biyar, sun kuma gano maboyar makamai

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda biyar, sun kuma gano maboyar makamai

- An gano maboyar makamai yayin bata kashin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan ta'adda biyar

- An kama mutane biyu da ake zargi masu safarar bindiga ne a jihar Sokoto tare da gano makamai da dama

- Rundunar soji ta bukaci yan Najeriya su taimakawa jami'an tsaro da bayanai don kakkabe ta'addanci a kasar

Rundunar Sojoji ta Lafiya Dole na Najeriya sun ce sun kashe 'yan ta'adda biyar tare da gano mabuyar makamai lokacin yakar ta'addanci a Arewa maso gabas.

An bayyana haka ne ranar Alhamis ta bakin mai kula da yada Labaran soji, Manjo Janar John Eneche lokacin da yake jawabi a Abuja kamar yadda The Channels ta ruwaito.

Sojoji sun kashe yan ta'adda biyar, sun kuma gano maboyar makamai
Sojoji sun kashe yan ta'adda biyar, sun kuma gano maboyar makamai. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya naɗa gwamnan Zamfara sarauta

Ya yi bayanin yadda sojoji ke ci gaba da dirarwa ayyukan yan tada kayar baya da masu ayyukan ta'addanci ana samun nasara.

"Rundunar mu ta kai hare hare kan maboyar yan ta'adda, kuma sun dawo da martani ga rundunar. A lokacin harin, karfin rundunar mu ya janyo kawar da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP.

"Kamar yadda muka sani, tsakanin 7 da 8 ga Nuwamba 2020, jami'an runduna ta 27 da ke barikin Buni Gari a karamar hukumar Gujba, jihar Yobe sun kashe yan ta'addan Boko Haram da ISWAP. A lokacin bata kashin an gano maboyar makamai da harsashi," a fadar sa.

KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Eneche ya kuma ce, a daya daga cikin atisayen da suka gudanar ranar 8 ga Nuwamba, jami'an atisayen sunyi amfani da basira wajen gano wasu da ake zargin masu safarar bindiga ne a Tangaza da ke jihar Sokoto.

Sun kuma kama mutane biyu da ake zargi, Abubakar Mohammad da Ansi Usman Janare da kuma kwato karamar bindiga mai sarrafa kanta, bindigu kirar AK47 guda hudu, da kananan harsashi guda 586, sai kuma harsashi na musamman guda 100 da kuma babur guda daya.

Ya kuma roki 'yan Najeriya da mazauna da su taimaka wajen mika bayanan da suka dace don taimakawa wajen kakkabe yan ta'adda daga kasar.

A wani labarin, wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu.

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel