TSA: Gwamnatin Bauchi ta bankado N1.48bn a wasu asusun bankuna 586
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce gwamnatinsa ta rufe asusun bankuna 586
- A cewarsa, an gano asusun suna da alaka da tsohuwar gwamnatin jihar, kuma a ajiye kawai suke
- Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a jiharsa, yayin taron horarwa na TSA
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce mulkinsa ya bankado N1.48 daga asusun bankunan mutane 586, sai wasu 265 boyayyu wadanda suke da alaka da tsohuwar gwamnatin jihar.
Yahaya ya bayyana hakan a Gombe ranar Alhamis yayin taron horarwa na TSA.
An shirya horarwar ne musamman don masu biyan albashi da kididdiga, shugabannin ma'aikatu da bangarori daban-daban na jami'o'i.
A cewarsa, tunda ya saka hannu a TSA, ya samu nasarori da dama, don an samu asusun banki masu hadi da gwamnatin jihar guda 2,292, sannan an kara bankado wasu 265.
A cewarsa, gwamnatinsa ta rufe asusun bankuna 586 wadanda ba a amfani da su, an ajiyesu ne kawai.
Ya kara da cewa, "A ce asusun bankuna 2,292 duk ba a amfani da su, ta yaya za a yi a samu ingancin kirga da kididdiga? Don haka wajibi ne mu yi wani abu akai."
Kamar yadda yace, matsawar ana son jiha ta cigaba, wajibi ne a yi gyara, ba a da wani zabi.
KU KARANTA: Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi
KU KARANTA: Mutuwar Balarabe Musa babbar asara ce ga Najeriya da damokaradiyya, Ganduje yace
A wani labari na daban, an tsinci gawar wata budurwa, mai kimanin shekaru 22 da haihuwa a wata kwata da take wurin layin Osumenyi/ Akwuihedi, anguwar Osumenyi da ke karamar hukumar Nnewi a jihar Anambra.
Gawar, wacce ba a gano sunanta ko adireshinta ba, an zargi kasheta aka yi. Wasu mutanen kirki ne suka ga gawar, da alamun shaka a wuyanta.
The Nation ta tattaro bayanan yadda aka yi amfani da rufe bakinta, sannan aka daure kafafunta da hannayenta da igiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng