Mutuwar Balarabe Musa babbar asara ce ga Najeriya da damokaradiyya, Ganduje yace
- Gwamna Ganduje na jihar Kano, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar jihar Kaduna a bisa babban rashin da sukayi
- Tun bayan jin labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Abdulkadir Balarabe, jama'a suke ta tura sakon ta'aziyyarsu
- A cewarsa, mutuwar tsohon gwamnan, babbar asara ce ga jihar Kaduna, demokradiyya da Najeriya gabadaya
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya bayyana mutuwar Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, a matsayin babbar asara ga Najeriya da demokradiyya.
Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, lokacin da yake mika sakon ta'aziyyarsa, Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda yace, "Mun samu wannan mummunan labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar Kaduna na farko a mulkin farar hula, Malam Abdulkadir Balarabe Musa, wanda ya rasu a lokacin da muka fi bukatarsa."
A cewarsa, "Marigayin ne da ire-irensa suka gyara jihar Kaduna. Mun karu kwarai da marigayin musamman a kan harkar siyasa."
KU KARANTA: Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya
KU KARANTA: 'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari
A cewar Gwamna Ganduje, "tsohon gwamnan ya tsaya tsayin-daka wurin taimakon talakawan da aka daura shi a kansu, yakamata ace irin ayyukan da yayi lokacin yana gwamna su tabbatar wa mutane da irin tausayin talakawansa da yake yi."
"A madadin gwamnatin jihar Kano da mutanen kirkin jihar, ina mai mika ta'aziyya ga iyalansa, gwamnatin jihar Kaduna, abokansa da masoyansa. Muna addu'ar Allah ya gafarta masa, ya kuma yafe masa kurakurensa," a cewarsa.
A wani labari na daban, bidiyon wata mata yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda take bayyana yadda take rabuwa da kawayenta idan ta gano basu da saurayi ko miji.
Kuma ta shawarci duk wasu masu soyayya ko aure, da su rabu da kawayensu marasa masoya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng