Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi

Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi

- Idan mutum yana raye, bai gama jin abubuwan mamaki ba

- Wani saurayi ya wallafa yadda budurwarsa ta yaudaresa a shafinsa na Twitter

- A cewarsa, ashe aure za ta yi, amma ta ki sanar da shi, sai ana saura kwana 4

Wani saurayi ya wallafa yadda zuciyarsa ta sosu a kan wani kalubale da ya fuskanta a soyayya.

Saurayin mai suna Skinnyniggr ya wallafa hotunan yadda ta kaya tsakaninsa da buduwarsa wacce yake mutukar kauna.

Budurwarsa ta tura masa sako, inda ta ke sanar da shi cewa saura kwanaki kadan a daura mata aure .

Wani Chimuanyarhs ya yi tsokaci a karkashin wallafar, inda yace shi ma ya fuskanci kalubale a soyayya.

KU KARANTA: Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure

A cewarsa, sun kai kusan shekara daya suna soyayya da budurwarsa, har ta je Legas wurinsa, suka yi satittuka tare.

Sai tayi tafiyarta, yayi ta neman ta na kwanaki 2, har yana kukan rashinta. Bayan kwana 4 ta tura masa sako, inda take sanar da shi cewa an sa ranar aurenta, shiyasa ta tafi.

Mutane da dama sun yi mamakin irin wannan yaudara da budurwar tayi masa, inda suka yi ta tsokaci.

Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi
Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi. Hoto daga @chimuanyarhs, Tiny Buddha
Asali: Twitter

Wani MAyiWA_zz ya ce gaskiya budurwar bata kyauta ba, har yake cewa shi dai ya hakura da soyayya.

Soulsurviver5 ya ce: "A rayuwar nan mata sun iya yaudara."

KU KARANTA: 'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari

A wani labari na daban, Hussaina Salisu, 'yar karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, ta ce cikin yaranta 15, ta haifi guda 13 ita kadai a gida.

Ta ce bata taba fuskantar wasu wahalhalu ba yayin haihuwar yaranta ba. A cewarta, "cikin yarana 15, guda 2 ne kadai na haifa a asibiti."

Matar, mai shekaru 54 ta ce ba za ta shawarci wata mace ta yi kwatankwacin abinda tayi ba, inda tace "Da ban samu wayewa ba, da yanzu ban tsinci kaina a halin da na ke ba a yanzu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng