An tsinci gawar budurwa mai shekaru 22 cikin kwata a jihar Anambra

An tsinci gawar budurwa mai shekaru 22 cikin kwata a jihar Anambra

- An tsinci gawar wata budurwa wacce ba za ta wuce shekaru 22 ba da haihuwa a jihar Anambra

- Wasu mutanen kirki ne suka kai wa 'yan sanda rahoto, bayan sun ga gawar a wata kwata a daddaure

- Kakakin hukumar 'yan sandan, Haruna Mohammed ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda ta ranar Laraba

An tsinci gawar wata budurwa, mai kimanin shekaru 22 da haihuwa a wata kwata da take wurin layin Osumenyi/ Akwuihedi, anguwar Osumenyi da ke karamar hukumar Nnewi a jihar Anambra.

Gawar, wacce ba a gano sunanta ko adireshinta ba, an zargi kasheta aka yi.

Wasu mutanen kirki ne suka ga gawar, da alamun shaka a wuyanta.

The Nation ta tattaro bayanan yadda aka yi amfani da rufe bakinta, sannan aka daure kafafunta da hannayenta da igiya.

Kakakin hukumar 'yan sanda, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ana cigaba da binciken wadanda suka yi wannan mummunan aikin.

A cewarsa: "A ranar 10 ga watan Nuwamban 2020, da misalin karfe 12 na rana, wasu mutanen kirki suka kawo rahoton tsintar gawar wata budurwa, wacce har yanzu ba a gano sunanta da adireshinta ba.

"Amma ba za ta wuce shekaru 22 da haihuwa ba, a cikin wata kwata a layin Osunenyi/Akwuihedi, da alamun shaketa aka yi a wuya, sannan an rufe bakinta, an kuma daure kafafuwa da hannayenta da igiya."

Sai da aka dauki hotunanta, sannan likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

KU KARANTA: Yadda budurwata tayi batan-dabo, daga baya ta sanar da ni an sa ranar aurenta, matashi

An tsinci gawar budurwa mai shekaru 22 cikin kwata a jihar Anambra
An tsinci gawar budurwa mai shekaru 22 cikin kwata a jihar Anambra. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya bayyana mutuwar Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, a matsayin babbar asara ga Najeriya da demokradiyya.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, lokacin da yake mika sakon ta'aziyyarsa, Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng