Tubabben Boko Haram ne ya halaka kanal din soja, Sanata Ndume
- Tubabbun 'yan Boko Haram ne suka yi sanadiyyar mutuwar Kanal D.C. Bako, cewar Sanatan jihar Borno, Ali Ndume
- Ndume ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, inda ya ce sam ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa
- Ya ce tubabbun 'yan Boko Haram su na cigaba da ta'addanci, don haka wajibi ne gwamnati ta daina tallafa musu tana fifita su
Tubabbun 'yan Boko Haram ne sukayi sanadin mutuwar kanal din sojojin kasa, Premium Times ta wallafa.
Tubabben dan Boko Haram ne yayi sanadin kisan wani Kanal na sojojin kasa, Kanal D.C Bako, a cewar sanatan jihar Borno, Ali Ndume.
A cewarsa, tubabben dan Boko Haram din ne ya bayar da bayanai a kan Kanal din.
An kashe Bako a ranar 21 ga watan Satumba a wani karon batta da suka yi da 'yan Boko Haram din, kusa da Damboa, wani gari da bai wuce kilomita 85 da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Bayan tabbatar da mutuwarsa, rundunar sojin kasa sun kwatanta D.C Bako a matsayin gwarzo kuma jarumin soja.
Ndume, wanda shine shugaban kwamitin sojojin kasa na majalisar dattawa, ya sanar da manema labarai hakan a ranar Laraba, bayan bayyana kasafin rundunar soji.
Sanatan ya amsa tambayar da aka yi masa a kan samar da kudade ga sojoji da kuma taimakon tubabbun 'yan Boko Haram da suka koma anguwanninsu.
Ya ce "Gaskiya ban amince da yafe wa tubabbun 'yan Boko Haram ba. Ba za a cigaba da fifita su ba a kan mutane. Na tabbatar da cewa mafi yawan 'yan Najeriya ba za su goyi bayan cigaba da tallafa musu ba.
"A kauyenmu, an saci malamai da manya akalla masu shekaru 60, kusan su 75. 'Yan Boko Haram suka kai su mayanka suka kashesu. Ta yaya za a yi a ce har yanzu Najeriya tana taimakon tubabbun 'yan Boko Haram?"
KU KARANTA: Duba garejin dan wasan kwallo Obafemi Martins, mai dauke da kasaitattun motocin kece raini
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yar kunan bakin wake tare da wasu mayakan ta'addanci
A wani labari na daban, al'amarin 'yan bindiga kullum kara faskara yake yi a jihar Zamfara. Don yanzu haka sun fara sanya wa manoma haraji kafin su yi girbi.
Wani Abdussalam Ibrahim Ahmed ya ce: "Yan bindiga sun umarcemu da mu biya N800,000 matsawar muna son su bar mu mu yi noma cikin kwanciyar hankali, kuma har mun biya."
Kamar yadda yace, sai da suka biya haraji kafin su bar su su yi girbi. Har yanzu, 'yan ta'adda suna cigaba da kashe-kashe, kai hare-hare, har da yi wa mata fyade a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng