Mijina ya yi min ƙaryar nice matarsa ta biyu, alhalin nice ta shida - Mata ta shaidawa kotu
- Kotu ta raba auren shekara hudu saboda kawo maslaha tsakanin mata da mijin
- Mijin ne ya shigar da kara kan a raba auren saboda matarsa ta na tayar masa da hankali
- An danka dansu daya a hannun matar tare da umartar mijin ya dinga bada 5,000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa
Wata kotun gargajiya a Ile-Tuntun, Ibadan, ranar Talata, ta raba auren shekara hudu tsakanin Alhaji Azeez Busari, da tsohuwar matarsa, Koasara akan cewa tana da saurin fushi.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Cif Henry Agbaje ya ce kotu baza ta zuba ido har abu ya kai ga zubda jini kafin ta dauki mataki akan kowace matsala ba.
Agbaje ya raba auren saboda a maslaha kuma ya bada dansu daya tilo ga Kaosora kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ya umarci Busari da ya biya 5,000 ga Koasara a matsayin kudin ciyarwa.
Ya kuma shawarci maza da mata da su dinga nutsuwa suna zabar abokan zama kafin akai ga aure.
DUBA WANNAN: Manyan 'yan siyasa sun hallarci ɗaurin auren ɗan Aliero da 'yar Yariman Bakura a Sokoto
Busari ne ya shigar da karar yana neman kotu ta raba auren saboda yadda matarsa take tayar masa da hankali.
"Watakila da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da na dauki mataki tun farko da na ga take taken ta. Kaosora shedaniya ce.
"Tana yunkurin kashe mahaifi na. Kaosora ta bayyana min irin halinta yayin da ta lalata kayan daki na da adda ta kuma nemi da muyi fada," a cewar Busari.
KU KARANTA: Harin Musulmin Ƙabilar Igbo: MURIC ta buƙaci a gurfanar da Rev Fr. Onah
Sai dai Kaosora ta karyata da yawa daga cikin zargin da ake mata kuma tace mijin nata neman mata yake.
"Kafin na aure shi, yayi min karya cewa matarsa daya, sai dai, matarsa ta farko ta shaida min cewa nice ta shida kuma tuni ya shirya auren hudu.
"Azeez ya auri mata biyu bayan ni, kuma yana asirce duk matar da ta bar gidansa ta yadda ba wanda zai sake aurenta," a cewarta.
An dai ga wani abin al'ajabi ranar 20 ga Oktoba bayan da Busari ya ki fita daga kotu yana ikirarin Kaosora ta kawo mutane don su doke shi.
A wani labarin, gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata ya sanar da niyyansa na soke dokar biyan fansho na 2007 da ke bada damar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho.
Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi na shekarar 2021 da Majalisar Jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng