'Yan fashi sun sace €6.5m daga ofishin kwastam a Jamus

'Yan fashi sun sace €6.5m daga ofishin kwastam a Jamus

- Wasu da ake zargin ƴan fashi ne sun afka ofishin kwastam a ƙasar Jamus

- Wadanda ake zargin sun sace zunzurutun kuɗi har fam miliyan 6.5 daga ma'ajin kuɗi

- Rundunar yan sandar ƙasar ta yi alkawarin bada la'adar Euro 100,000 ga wanda zai bada bayani a kansu

Masu bincike a kasar Jamus a ranar Laraba sun ce sun fara bincike kan wasu da ake zargin sun sace fam miliyan 6.5 daga ofishin kwastam a ƙasar.

"An yi amfani da dabaru irin na ƙwararru yayin satar: uku cikin wadanda a yanzu ba a gano su ba sunyi amfani da na'urar huda abubuwa wurin shiga inda ake ajiye kuɗin," a cewar ƴan sanda.

'Yan fashi sun sace fam miliyan 6.5 daga ofishin kwastam a Jamus
'Yan fashi sun sace fam miliyan 6.5 daga ofishin kwastam a Jamus. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

An yi satar ne a ofishin kwastam da ke yammacin birnin Duisburg a ranar Lahadi 1 ga watan Nuwamba kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wasu ganau sun ce sun ji hayaniya misalin ƙarfe 6 na safe. Bayan awa uku kuma sun hangi mutane sanya da baƙaƙen kaya da huluna sun shiga ginin sun fito da jakunkuna sun saka a wata farar mota.

Daga bisani suka tafi a cikin motar.

KU KARANTA: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Wani shaidan ganin idon ya ce ya hangi wani mutum yana zagaye a ofishin na kwastam daga bisani ya shiga mota ya bi farar motar.

Ƴan sanda sun wallafa hotunan da shaidun suka ɗauka na mutanen tare da alƙawarin bada la'adar Euro 100,000 ga duk wanda ya bada bayanin da ya yi sanadin kama wanda ake zargin.

A wani labarn, wata kotun gargajiya a Ile-Tuntun, Ibadan, ranar Talata, ta raba auren shekara hudu tsakanin Alhaji Azeez Busari, da tsohuwar matarsa, Koasara akan cewa tana da saurin fushi.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Cif Henry Agbaje ya ce kotu baza ta zuba ido har abu ya kai ga zubda jini kafin ta dauki mataki akan kowace matsala ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel