An yi jana'izar marigayi Alhaji Balarabe Musa a Kaduna (Hotuna)

An yi jana'izar marigayi Alhaji Balarabe Musa a Kaduna (Hotuna)

- An yi jana'izar tsohon gwamnan Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa a Ungwan Sarki Kaduna

- Cikin wadanda suka hallarci jana'izar akwai Sanata Shehu Sani da tsaffin gwamnonin Kaduna, Ramalan Yero, Ahmed Makarfi

- Marigayin ya rasu yana da shekaru 84 a duniya ya kuma bar yara da jikoki

An yau Laraba 11 ga watan Nuwamba ne aka yi jana'izar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a garin Kaduna.

Ya rasu sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Laraba yana a gidansa ke Ungwan Sarki a Kaduna.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 84 a duniya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna)
An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna). Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna)
An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna). Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna)
An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna). Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

An yi jana'izarsa a maƙabartar Ungwan Sarki misalin ƙarfe 5 bayan an masa salla a masallacin Sultan Bello da ke Ungwan Sarki a Kaduna.

Ungwan Sarki na karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ne a jihar.

Manyan mutane da ƴan siyasa dama sun hallarci jana'izar ciki har da tsaffin gwamnonin jihar Kaduna Ramalan Yero da Ahmed Makarfi.

Saura sun haɗa da Babban Alƙalin Jihar Kaduna, Mai Shari'a Mohammed Lawal, ɗan takarar gwamnan PDP a zaben 2019, Hon Ishah Mohammed Ashiru da kwamishinoni da hakimai.

An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna)
An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna). Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Gwamna Nasiru El-Rufai bai samu hallartar jana'izar ba domin baya kasar amma sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas Lawal ya wakilce shi.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kazeem ya ce zai rika tuna mahaifinsa a matsayin "mutum mai ƙaunar talakawa kuma ya bani tarbiyya tare da koyar da ni rayuwar duniya. Ina kuma son irin siyasarsa.

"Mutum ne mai gaskiya kuma baya ɓoye-ɓoye."

An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna)
An yi jana'izar Balare Musa a Kaduna (Hotuna). Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

A wani labarin, An samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel