Balarabe ya rasu ne sakamakon bugun zuciya, dan gidan marigayin

Balarabe ya rasu ne sakamakon bugun zuciya, dan gidan marigayin

- Za'a yi Jana'izar marigayi tsohon gwamnan Kaduna a Masallacin Sultan Bello

- Balarabe Musa ya yi fama da rashin lafiya gabanin rasuwarsa

- Wasu manya sun kai shi asibiti kasar waje yayinda ciwonsa yayi tsanani, cewar 'dansa

Daya daga cikin yaran marigayi Balarabe Musa, AbdulKasim Balarabe Musa, ya ce mahaifinsa ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

A hirar da yayi da jaridar Tribune, yace "tsawon wani lokaci yanzu mahaifi na na fama da matsala da zuciyarsa."

"Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero da wasu sun kai shi kasar waje domin jinyarsa amma tun daga lokacin, bai samu sauki ba, " yace.

"Mun ji dadi ya rasu da safen nan (Laraba) cikin baccinsa misalin karfe 8 na safe."

AbdulKasim wanda yayi takarar kujerar majalisar wakilai ta Kaduna North a 2019, ya ce zasu yi rahsin mahaifinsu.

Bayan haka, shugaban jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP), Alh Abdulrahaman Haruna, ya ce za'ayi jana'izarsa a Masallacin Sultan Bello misalin karfe 4 na la'asar.

KU KARANTA: Allah ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna, Balarabe Musa rasuwa

Balarabe ya rasu sakamakon bugun zuciya, za'a yi janaizarsa bayan La'asar
Balarabe ya rasu sakamakon bugun zuciya, za'a yi janaizarsa bayan La'asar Hoto: @thisdaylive
Asali: Twitter

KU DUBA: 2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi

Marigayi Abdulkadir Balarabe Musa ya kasance tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jagoran jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP).

An haifeshi 1936, Balarabe Musa ya zama gwamnan tsohuwar jihar Kaduna (Katsina da Kaduna) a 1979.

Mambobin jam'iyyar NPN na majalisar dokokin jihar sun tsigeshi daga mulki ranar 23 ga Yuni, 1981.

Yan Najeriya a gida da waje sun aika sakonni ta'aziyyarsu ga iyalan Balarabe da gwamnatin jihar.

Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani shima ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba.

A sakon da ya wallafa a Twitter, Shehu Sani ya rubuta "Alhaji Balarabe Musa ya rasu a yau. Allah ya jikan rai ya kuma saka masa da gidan Aljanna Firdausi. Amin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel