Da duminsa: Jigo a fadar Buhari ya rasu sakamakon ciwon kansa
- Fadar shugaban kasa ta fada alhini da makokin rasuwar Babatunde Lawal sakamakon ciwon kansa
- Lawal mai shekaru 56 ya rasu a ranar Juma'a, 6 ga watan Nuwamba, bayan shekaru biyu da nada shi babban sakatare
- A sakon ta'aziyyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya kwatanta mutuwar Lawal da ikon Allah
Babatunde Lawal, babban sakataren a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya rasu.
Lawal ya rasu a ranar Juma'a, 6 ga watan Nuwamba bayan fama da cutar kansar hanta da yayi. Ya rasu bayan daukar shekaru biyu da yayi a kan mukaminsa.
Masani ne a fannin tattalin arziki tare da tsari. Ya fara aiki da gwamnatin tarayya a watan Oktoban 1987 a matsayin jami'in tsari a ma'aikatar tsari da tattali ta tarayya.
Mamacin ya yi aiki a wurare da dama wadanda suka hada da mamba a kwamitin asusun tarayya da kuma kudin shiga kuma yayi aiki da NBS.
A daya bangaren, SGF Mustapha ya nuna damuwarsa tare da alhininsa a kan mutuwar Lawal, ya kwatanta rasuwarsa da ikon Allah.
A wata takarda da babban sakataren ofishin SGF ya fitar, Maurice Nnamdi Mbaeri, Mustapha ya ce ya matukar damuwa da mutuwar Lawal.
KU KARANTA: Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci
KU KARANTA: Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yanke hukunci
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta sanin masu hada hotunansa a fosta da sunan kamfen dinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 dake gabatowa.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan haduwarsa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ranar Juma'a.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng