Karen Biden, zababben shugaban Amurka zai kafa babban tarihi a duniya

Karen Biden, zababben shugaban Amurka zai kafa babban tarihi a duniya

- Major, shine kare na farko da zai fara rayuwa a White House

- Dama karen ya samu shakuwa kwarai da iyalin Joe Biden

- Ga dukkan alamu, Joe Biden ba zai bar karensa a baya ba

Major, karen Joe Biden ne dabba na farko mara gata da zai fara rayuwa a cikin white house, The Cable ta wallafa.

Ana sa ran karen dan asalin kasar Jamus zai koma rayuwarsa tare da Biden da Jill, matarsa da zarar an rantsar dashi sun koma White House.

Kamar yadda Sky News suka ruwaito, ba wannan ne karo na farko da kare ya fara rayuwa a White House ba, Major ne kare na farko wanda aka dauko daga makwancin karnuka da zai zauna a nan.

Champ ya fara rayuwa tare da iyalin Biden a 2008, shekarar da ya zama mataimakin shugaban kasa Barack Obama.

A 2018, diyar Biden, Ashley ta ga hotunan Major da wata kungiya mai kula da makwancin karnuka na Delaware ta wallafa hotunan kare a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, tun lokacin yana karami sosai.

Bayan nan ne Biden ya nemi a kawo masa karen, ya kawo shi gida don ya cigaba da zama tare da iyalinsa.

A ranar 1 ga watan Nuwamba, Biden yayi wata wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace "Mu mayar da karnuka White House."

Daga ganin wannan wallafar ne mutane suka yi ta cewa akwai alamun cewa har da Major, Biden zai tafi White House.

KU KARANTA: Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara

Karen Biden, zababben shugaban Amurka zai kafa babban tarihi a duniya
Karen Biden, zababben shugaban Amurka zai kafa babban tarihi a duniya. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)

A wani labari na daban, Melania, matar Trump tana neman sakinsa, mintina kadan da shan kayensa, cewar tsohuwar hadimar Trump, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda rahotonni suka bayyana, tsohuwar hadimar Trump ta ce Melania na neman sakin mijinta bayan ya fita daga White house.

Kamar yadda tsohuwar hadimar Trump din tace, matarsa na jiran lokacin da za su kwashe ya-nasu ya-nasu su bar gidan gwamnati, ita kuma za ta sake shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel