An sako ɗan uwan tsohon Sarkin Kano Sanusi da aka yi garkuwa da shi

An sako ɗan uwan tsohon Sarkin Kano Sanusi da aka yi garkuwa da shi

- Masu garkuwa da mutane sun sako Aminu Musa Abdaullahi dan uwan tsohon sarki Muhammadu Sanusi II

- Hakan na zuwa ne bayan ya yi kwanaki hudu a hannun masu garkuwar da suka sace shi a hanyar Abuja zuwa Kaduna

- An sako shi a daren ranar Lahadi kamar yadda wata majiya daga iyalan gidan ta sanar kuma ba a san ko an biya kudin fansa ba

An sako Aminu Musa Abdullahi dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga hannun masu garkuwa.

An sace shi ne a hanyar babban birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna a makon da ta gabata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An sako dan uwan tsohon Sarkin Kano Sanusi da aka yi garkuwa da shi
Sarki Muhammadu Buhari. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Manyan 'yan siyasa sun hallarci ɗaurin auren ɗan Aliero da 'yar Yariman Bakura a Sokoto

Wata majiya na kusa da iyalan tsohon sarkin ta ce Abdullahi da aka fi sani da Yaya Baba ya dawo gida bayan shafe kwanaki hudu a hannun masu garkuwa.

Ya dawo cikin koshin lafiya a daren ranar Lahadi kamar yadda majiyar ta bayyana.

A halin yanzu ba a tabbatar ko an biya kudin fansa kafin a sako shi ba ko kuma ba a biya ba.

KU KARANTA: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

A wani labarin, kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci a kama kuma a gurfanar da Rev. Fr. Godfrey Igwebuike Onah, wata huduba da ya yi a coci na tunzura matasan kiristoci a Nsukka, jihar Enugu, da su kai hari kan musulmai da kuma lalata masallatai a garin.

Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, wanda ya yi wannan batun a ranar Juma'a a wata sanarwa, ya ce kungiyar ta goyi bayan Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) a karar da ta shigarwa DSS na a kama tare da gurfanar da Rev. Onah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel