Zaben Amurka: Melania ta goyi bayan Trump, ta ce 'dole a kirga duk wata halastaciyyar kuri'a'

Zaben Amurka: Melania ta goyi bayan Trump, ta ce 'dole a kirga duk wata halastaciyyar kuri'a'

- Daga karshe, mai dakin shugaban Amurka Melania Trump ta yi magana game da zaben Amurka

- Misis Trump, a jawabin da ta wallafa a Twitter ta ce 'ya zama dole a kirga dukkan kuri'a ta halas'

- Hakan na nuna cewa har yanzu tana goyon bayan mai gidanta Donald Trump kan ikirarinsa na cewa an tafka magudi a zaben

Uwargida shugaba Donald Trump na Amurka, Melania Trump ta ce ya zama dole Amurkawa su kare demokradiyyarsu.

Misis Trump ta yi jawabi ta hanyar amfani da shafinta na Twitter yayin da ta ke martani a kan zaben shugaban kasa da aka kammala a kasar a baya bayan nan.

Zaben Amurka: Melania ta goyi bayan Trump, ta ce 'dole a kirga duk wata halastaciyyar kuri'a'
Melania Trump: Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

Wannan shine jawabi na farko da Mrs Trump ta yi tun bayan nasarar Mr Joe Biden.

Idan za a iya tunawa Donald Trump da lauyoyinsa sun shirya kararraki da za su shigar a kotu kan zargin magudin zabe da suka ce anyi kamar yadda ya fadi a talabijin.

Mrs Trump daga karshe ta yi magana a game da zaben na Amurka ta nuna cewa har yanzu tana goyon bayan mai gidanta da ikirarin da ya yi a Twitter na cewa an tafka magudi a zaben.

KU KARANTA: Manyan 'yan siyasa sun hallarci ɗaurin auren ɗan Aliero da 'yar Yariman Bakura a Sokoto

Ta rubuta cewa: "Zaben adalci da gaskiya ya kamata a yi wa Amurkawa. Dole a kirga dukkan halastaccen kuri'a - banda haramtacce. Ya zama dole mu kare demokradiyyar mu da gaskiya ba tare da rufa-rufa ba."

A wani labarin, barayi sun sace kaya masu tsada da kudinsu ya kai Euro 600,000 daga gidan 'yar gidan sarautar Saudiyya da ke kasar Faransa kamar yadda wani na kusa da masu bincike ya sanar a ranar Juma'a.

'Yar gidan sarautar mai shekaru 47 ba ta shiga gidan ba tun watan Agusta amma da shigar ta sai ta gano an ce mata jakkuna, agoguna, kayan ado na zinari da wasu tufafin da kudinsu ya kai Dallar Amurka 720,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel