Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yanke hukunci

Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yanke hukunci

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zanga-zangar EndSARS tana nuna harzukar matasan Najeriya

- Don haka, wajibi ne a dinga sauraron matasa kafin a dauki wani hukunci a kasa don an lura da illar rashin yin hakan

- Shugaban kasar, ya samu wakilcin shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Gambari a ranar Lahadi a jihar Legas inda ya sanar hakan

Shugaba Buhari ya ce rikicin EndSARS alama ce ta fusatar matasan Najeriya.

A watan Oktoba, 'yan Najeriya da dama sun yi ta zanga-zanga a tituna suna bukatar a gyara lamarin 'yan sanda. The Cable ta wallafa.

Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Gambari ya roki gwamnonin kudu maso yamma da su yi gaggawar gyara al'amarin tun daga tushe.

Shugaban kasar ya ce ba maganar fatar baki ya kamata shugabanni su tsaya yi ba, ya kamata su samar wa da matasa ayyukan hannu.

KU KARANTA: Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yake hukunci
Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yake hukunci. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa

A cewarsa "Da idanunmu mun ga yadda zanga-zangar lumana ta koma hargitsi da tashin hankali, wanda hakan ya rikitar da dukkaninmu.

"Abinda muka gani alama ce da ke nuna ya kamata mu yi hobbasa mu kawo gyara. Wajibi ne mu tabbatar mun samar da zaman lafiya duk tsanani duk rintsi."

Ooni ya ce zai samar da wata gaba, wacce za ta hada shugabannin gargajiya wuri guda idan matsala irin wannan ta taso, don a yi gaggawar dakatar da ita.

A wani labari na daban, jaridar Leadership ta wallafa cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya wadanda har ya zuwa yanzun basu lashi romon gwamnatinsa ba, da kuma wadanda su ke ganin gazawar gwamnatin, da su yi hakuri.

Ya yi wannan roko a ranar Juma'a a garin Ilorin a wurin taron fadi-ra'ayinka. Taron wanda an yi shi ne saboda zanga-zangar EndSARS da kuma sakamakon da ta haifar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel