Gara a rasa mulki amma a tsira da mutunci - Jonathan

Gara a rasa mulki amma a tsira da mutunci - Jonathan

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce zai fi idan mutum ya rasa mulki amma ya tsira da mutuncinsa

- Kamar yadda ya wallafa a kafar sada zumuntar zamni ta Facebook, Jonathan ya ce a hakan ya ginu kuma ya ke kira ga shugabannin duniya da su ginu a kai

- Ya kara da cewa, a duk lokacin da wani kalubale ya tunkaro shugaba, kamata yayi ya duba mutuncinsa farko kafin ya duba wani buri nasa na mulki

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce gara mutum ya rasa mulki amma ya tsira da mtuncinsa, jaridar The Punch ta wallafa.

Jonathan ya sanar da hakan ne a wata wallafa da yayi a kafar sada zumuntar zamani a ranar Juma'a inda ya ce hakan ya kamata dukkan masu mulki su duba a yayin da suke fuskantar kalube a yayin zabe.

Ya wallafa, "Babu wanda burinsa ya kai darajar jinin dan kasa. Gara mutum ya rasa mulki a kan ya dage sai ya samesa ta kowacce hanya sannan ya rasa darajarsa.

"A kowanne lokaci, kwadayin mulki bai kamata ya zarce kaunar jama'a ba. Wannan shine abinda nayi dogaro da shi kuma na rayu da shi.

"Na tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasata ta gado da kuma ni kaina. Wannan nake kira ga sauran shugabanni da su duba a dukkan lokutan da suke fuskantar kalubale na gwamnati da kuma mu'amala da masu siyasa."

Jonathan wanda ya nemi zarcewa a karo na biyu a karkashin jam'iyyar PDP ya sha mugun kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a karkashin jam'iyyar APC.

Duk da Jonathan bai fito ya bayyana da wanda yake ba a cikin shugabanni, babu shakka yana maganar ne a kan zaben kasar Amurka da ke gudana a halin yanzu inda Donald Trump ke son zarcewa.

KU KARANTA: Katsina: Gwamnati ta rufe dukkan sansanin 'yan gudun hijira, ta mayar da mutum 27,000 gida

Gara a rasa mulki a tsira amma a tsira da mutunci - Jonathan
Gara a rasa mulki a tsira amma a tsira da mutunci - Jonathan. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

A wani labari na daban, a ranar Laraba, tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, ya bayyana dalilin da yasa ya goyi bayan takarar Alhaji Shehu Musa Yar'Adua a kan na Chief Olu Falae a shekarar 1992, yayin shirin zaben shugaban kasa na 1993.

Obasanjo, ya tunatar da hakan ne a lokacin kaddamar da tarihin rayuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, littafin Otunba Adebayo Alao-Akala, mai taken: "Amazing Grace," a cewarsa duka 'yan siyasan mataimakansa ne na kusa, a lokacin yana shugaban kasa na mulkin soji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel