Ku mayar da hankali kan matsalolin kasa ba Rahama Sadau ba - Reno Omokri
- Reno Omokri ya caccaki 'yan arewa a kan yadda suka yi ta sukar Rahama Sadau saboda hotunan tsiraicinta
- Ya ce maimakon su caccaki 'yan siyasa masu satar dukiyar al'umma amma sun mayar da hankali a kan jarumar
- A cewarsa, akwai matsaloli da dama da yakamata a ce an mayar da hankali, amma an dage wurin caccakar Rahama
Reno Omokri ya yi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya caccaki musulmai a kan zagin Rahama Sadau saboda rigarta mai bayyana tsirarici, amma suka yi shiru a kan satar da 'yan siyasa suke yi.
Reno ya wallafa hotunan musulmai mata da suke wasu kasashen, inda ya rubuta;
"Yan Najeriya, wadannan hotunan mata musulmai ne daga kasar Egypt, Pakistan da Lebanon. Kuna tunanin abinda Rahama Sadau ta aikata ya tsananta? Daga Musulunci har addinin Kirista bai halasta sata ba, amma muna alfahari da barayi.
"Mun saka wa wani filin wasa sunan wani babban barawo. A wannan jihar dai, an ga gwamna a kamara yana amsar rashawa ta daloli. Bai kamata a ce mu nuna takaicinmu a kansa ba, sai Rahama?
"Ta yaya za a ji dadin zaman duniya, idan muka kyale Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma mutane miliyan 13 da basu zuwa makaranta a arewacin Najeriya, amma mun mayar da hankali a kan shigar Rahama Sadau?"
Rahama ta fuskanci caccaka daga mutanen arewa a kafar zumuntar zamani ta Twitter makon da ya gabata, saboda bayyanar hotunanta masu bayyana tsiraicin ta. Yanzu haka hukumar shirya fina-finai ta MOPPAN ta dakatar da ita saboda bayyanar hotunan na ta.
KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa
KU KARANTA: Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa babagana Zulum, a ranar Juma'a ya ce shawo kan matsalar tsaro ta hanyar amfani da dakarun soji a kasar nan ba hanya ce mai bullewa ba ga matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso gabas.
Ya ce amfani da salon siyasa wurin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar shine hanya da ta dace, Vanguard ta ruwaito.
Farfesa Zulum ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labaran gidan gwwamnati bayan taron sirrin da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng