Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince

Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince

- Wani mutum mai suna Mlekeleli Masondo ya bayyana yadda ya gano matarsa tana ha'intarsa

- A cewarsa, yayi amfani da sunan bogi, inda suka yi ta soyayya da matarsa a tunaninta wani ne daban

- Ya ce, ya bukaci ta hana mijinta hakkin aurensa, yadda zai kwashi gara idan sun hadu, kuma ta amince

Wani mutum mai suna Mlekeleli Masondo, dan asalin South Africa, ya yi wata wallafa a shafinsa na Facebook, ta yadda yayi amfani da shafin bogi na kafar sada zumuntar zamani, har ya gano matarsa tana ha'intarsa.

Kamar yadda Masondo ya wallafa, ya yi amfani da sunan bogi, har matarsa ta amince da za su fita yawon shakatawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce ta dade tana hanasa hakkinsa na aure domin ta tattala wa saurayinta, ya kwashi gara a ranar farko da za su hadu.

KU KARANTA: Gara a rasa mulki amma a tsira da mutunci - Jonathan

Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince
Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince. Hoto daga Mlekeleli Masondo
Asali: Facebook

Mutumin ya ba wa maza da dama dabarar gano idan matansu suna ha'intarsu.

Masondo ya bayyana yadda suka yi ta sheke aya da matarsa a kafar sada zumunta amma bata san cewa shine ba.

Ya ce da zarar ya tafi aiki, sai matar ta tsunduma da soyayya da saurayin, a tunaninta wani ne ba shi ba, har tana tura masa kudi.

Kamar yadda ya wallafa, "Mata ta ta hadu da wani a Facebook, inda suka fara soyayya na tsawon sati 4. Gayen baya aiki, da zarar na tafi aiki, sai su fara hirar soyayya, har kudi take tura masa."

Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince
Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince. Hoto daga Mlekeleli Masondo
Asali: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram

Ya bayyana yadda matarsa tayi masa karyar cewa tana bukatar kudi don ta tura wa kanwar mahaifiyarta da ke fama da ciwo, amma ta tura kudin ga saurayinta.

Ya ce ta bayyana wa saurayin cewa babu abinda ta nema ta rasa, kawai tana kwasar nishadi ne.

Ya ce saurayin ya bukaci ta hana mijinta hakkin aurensa, saboda ya samu ya kwashi gara ranar da za su hadu, kuma ta amince da hakan.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci manyan ma'aikatan gwamnati zuwa wurare daban-daban a cikin kasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da matasa suka bukaci a yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da shugabannin gargajiya a kan matsalolin da Najeriya take fama da su, daga Daily Nigerian.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng