Gagarumin dan fashi da makami, Rambo, da aka dade ana nema ya bayyana, ya ce ya tuba

Gagarumin dan fashi da makami, Rambo, da aka dade ana nema ya bayyana, ya ce ya tuba

- Daya daga cikin gagaruman 'yan fashin da ake nema ruwa-a-jallo, Shina Rambo, ya tuba ya koma wa'azi don kira ga addinin Allah

- A cewarsa ya yi nadamar rasa matarsa da yaransa 3 a rana daya sakamakon nemansa da aka je yi baya nan aka kashe su

- Ya ce a lokacin yana hatsabibi, yana da asirai 901, wadanda suke bashi damar zama ko wanne irin halitta, sannan ya bace take-yanke

Daya daga cikin manyan 'yan fashin Najeriya, Shina Rambo, ya bayyana a babban birnin Ekiti, yana cewa shifa ya canja, yanzu haka ya koma kira ga addinin Kirista.

Ya yi wannan maganar ranar Lahadi a wani shiri na karshen mako da gidan rediyon Fresh FM, da ke Ado Ekiti, kuma dama shirin babban mawakin yabo ne, sannan mai gidan rediyon da kansa, Yinka Ayefele.

Rambo, wanda ya sanar da sunansa na asali Oluwasina Oluwagbemiga, ya ce shi din dai da ya dade yana addabar wasu bangarori na Najeriya tsawon lokaci, sannan ya kai hare-hare, ya yi kashe-kashe da tayar da hankula amma yanzu ya tuba.

Ya ce tabbas ya san mutane, musamman 'yan sanda, za su yi mamakin jin mutumin da ya dade yana kashe-kashe da barna, yau ace ya tuba.

Yayi ikirarin zama mai wa'azi, sannan ya canja daga munanan halayensa, Daily Nigerian ta tabbatar.

An haifi Rambo a shekarar 1958, sannan haifaffen Abeokuta ne, babban birnin jihar Ogun, amma ya taso a birnin Benin.

A cewarsa, "Mahaifina mutumin kirki ne sannan soja, ya yawata wuri-wuri a kasar nan, sakamakon yanayin aikinsa. Ni kuma na yi amfani da wannan damar naje wurare 21 saboda asire-asire, wadanda suka hada da Minna, jihar Niger da Oro, wacce yanzu ake kira Kwara.

"Na taba zama a Idanre, jihar Ogun na tsawon kwanaki 91, inda aka umarcemu da mu dinga tsotson nonon wata mahaukaciya a matsayin abincinmu kuma abin shan mu, saboda mu samu wani asiri.

"A karshen wannan asirin, na samu lakani 901, wadanda nake iya bacewa idan ana bi na, sannan ina iya bayyanar da hoton mutum duk lokacin da na so. Idan na ga za a kashe ni, ina da asirin komawa wani abu na daban take-yanke."

NAN sun ruwaito yadda yayi nadamar hatsabibanci da asire-asiren da yayi na tsawon lokaci. Ya ce ya tuba kuma ya koma mai wa'azi. Yana magana yana janyo ayoyin Bibul.

Rambo ya ce babban nadamar rayuwarsa shine rasa matarsa da yaransa 3 a rana daya, inda wadanda suka je nemansa amma basu same shi ba, suka kashe su.

KU KARANTA: Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Gagarumin dan fashi da makami, Rambo, da aka dade ana nema ya bayyana, ya ce ya tuba
Gagarumin dan fashi da makami, Rambo, da aka dade ana nema ya bayyana, ya ce ya tuba. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kun zabeni, kun karrama ni - Biden ya daukar wa Amurkawa muhimmin alkawari

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel