Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna

Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna

- Dakarun sojin Najeriya na ci gaba da samun manyan nasarori a bangaren tabbatar tsaro

- Hedkwatar tsaro ta kasa ta wallafa bidiyon ragargazar da sojin sama suka yi wa 'yan bindiga a Kaduna

- Kamar yadda aka gani, 'yan bindigar sun kwaso shanu daruruwa yayin da suke yunkurin barin dajin Kuzo

Dakarun sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta ta jirgin yaki a yankin Kuzo da ke jihar Kaduna.

Rundunar karkashin Operation Thunder Strike ta tabbatar da kisan 'yan bindiga masu yawa a wannan samamen da ta kai.

Kamar yadda bidiyon da hedkwatar tsaro ta wallafa a shafinta na Twitter ya bayyana, sojin saman ta jiragen yaki sun tare 'yan bindigar a Kuzo yayin da suke kokarin fitar da shanun sata daga dajin.

An ga 'yan bindigan suna yunkurin fitar da daruruwan shanu daga dajin a ranar 7 ga watan Nuwamban 2020.

Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya bayyana, an hango 'yan bindigar ta bangaren gabas maso yammacin dajin sannan sojin suka yi musu ruwan wuta.

Hakan yayi sanadin mutuwar 'yan bindigan masu tarin yawa a take.

KU KARANTA: Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna
Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: UGC

KU KARANTA: Takunkumi a kan Musulmin duniya: Biden ya sha alwashin warwaresu a take

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel