Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano

Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano

- Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta samu nasarar fasa kwalaben giya 1,975,000 masu kimar naira miliyan 200

- Hukumar ta yi hakan ne cikin shirin dakatar da rashin da'a a jihar, domin giya haramun ce a musulunci

- Gwamnan jihar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa ya ce za su tabbatar da inganta albashin hukumar

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta fasa kwalaben giya 1,975,000 mai kimar naira miliyan 200 a cikin tsakiyar jihar Kano, Daily Trust ta wallafa hakan a ranar Lahadi.

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna, yayin fasa kwalaben giyan a Kalebawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce shan giya zai iya janyo matsala ga kwakwalwar mutum, sannan Musulunci ya haramta.

Gawuna ya ce daya daga cikin rawar da mulkinsu zai taka shine tabbatar da walwalar 'yan Hisbah kafin karshen 2020, za a tabbatar an kara musu albashi sannan an samar mu su da sababbin kayan aiki.

"Mulkina yana alfahari da yadda ku ke jajircewa a kan ayyukanku. Don haka za mu yi iyakar kokarin ganin mun ba ku kwarin guiwa don cigaba da ayyukanku," cewarsa.

A jawabin kwamanda janar na hukumar Hisbah, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya ce hukumar ta samu nasarar lalata motoci 20 wadanda suke makil da giya.

Yayin da Ibn Sina ya bayyana farin cikinsa a kan yadda gwamnatin jihar take basu kwarin guiwa, ya tabbatar da cewa Hisbah ba za ta sassauta ba wurin yaki da rashin da'a a unguwanni.

Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano
Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5

Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano
Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano
Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu

Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano
Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng