Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno

Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno

- Rundunar Operation Lafiya Dole sun tarwatsa ma'adanar man fetur na mayakan ISWAP

- A cikin hakan ne suka yi nasarar ragargaza wasu daga cikin mayakan ta'addancin masu yawa

- Dakarun sojin sun kai samamen ta jiragen yaki ne a Tumbun Allura da ke jihar Borno

Dakarun rundunar Operation Lafiya Dole, sun tarwatsa wurin adana man fetur na mayakan ta'addanci na ISWAP a Borno.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa bidiyon, an ga jirgin saman sojin suna tarwatsa ma'adanar man a Tumbun Allura da ke Borno.

A cikin wannan kokarin na dakarun sojin saman ne suka samu halaka wasu mayakan ta'addancin masu yawa.

Kamar yadda aka sani, mayakan ta'addanci na ISWAP da Boko Haram sun dade suna cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Amma kuma, dakarun sojin sun jajirce inda suke cigaba da assasa tabbatar da tsaro a yankunan.

KU KARANTA: Sarkin Zazzau zai karba ma'aikatan fadarsa bayan mika masa sandan sarauta

Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno
Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

A wani labari na daban, Sufeta janar na 'yan sanda Adamu Mohammed, ya shawarci 'yan sanda da su yi amfani da makamansu a duk lokacin da su ka fuskanci wani hatsari, jaridar The Nation ta wallafa.

Sufetan ya bayar da wannan shawara ne a 'yan kwanakin nan yayin da ya ke yin jawabi ga jami'an 'yan sanda. A halin yanzun, Adamu ya na tafiye-tafiye zuwa jihohi daban-daban domin duba irin barnar da bata-gari su ka yi ga hukumar ta 'yan sanda a lokacin zanga-zanga ta EndSARS.

Rahotonni sun nuna cewar 'yan sanda da dama sun rasa rayukansu, an kuma barnata ofisoshin na 'yan sanda tarin masu yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: