Sarkin Zazzau zai karba ma'aikatan fadarsa bayan mika masa sandan sarauta

Sarkin Zazzau zai karba ma'aikatan fadarsa bayan mika masa sandan sarauta

- Sabon sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu, zai karbi ma'aikatan fadarsa yau, yayin nadinsa

- Kamar yadda rahotonni suka gabata, ana sa ran Gwamna El-Rufai ne zai ba wa sarkin sandar mulki

- Ana kyautata zaton manyan mutane daga wurare daban-daban za su halarci nadin sarautar

Sabon sarkin Zazzau, ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, zai karbi ma'aikatan fada yau a wurin bikin nadin sarautarsa da za a yi a filin Muhammadu Aminu (filin Polon Zaria) da ke jihar Kaduna.

Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ake kyautata zaton zai gabatar da sandar mulkin Zazzau ga sabon sarkin duk a cikin nadin.

Ana sa ran ganin manyan mutane daga wurare daban-daban da ke kasar nan, wurin nadin basarake na 19 na masarautar Zazzau mai dumbin da tarihi.

Sarkin Zazzau zai karba ma'aikatan fadarsa bayan mika masa sandan sarauta
Sarkin Zazzau zai karba ma'aikatan fadarsa bayan mika masa sandan sarauta. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Dama gwamnan jihar, El-Rufai ya nada sabon sarkin a ranar 7 ga watan Oktoban 2020, bayan rasuwar sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris, wanda ya mulki masarautar na tsawon shekaru 45.

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram

Wakilinmu, ya bayyana yadda El-Rufai ya nemi shawarar masu nadin sarki guda 5, kafin ya nada sabon sarkin.

Manyan masu sarautar Zazzau kamar Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru da Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris, sun kai wa sabon sarkin ziyara ta musamman don yin mubaya'a, amma Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, wanda ya zama na gaba yayin zabar sarkin, ya garzaya kotu don nuna rashin amincewarsa da nadin.

Alhaji Aminu ya ce zabar sabon sarkin ya sabawa al'ada da dokar masarautar.

KU KARANTA: Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare

A wani labari na daban, jaridar Leadership ta wallafa cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya wadanda har ya zuwa yanzun basu lashi romon gwamnatinsa ba, da kuma wadanda su ke ganin gazawar gwamnatin, da su yi hakuri.

Ya yi wannan roko a ranar Juma'a a garin Ilorin a wurin taron fadi-ra'ayinka. Taron wanda an yi shi ne saboda zanga-zangar EndSARS da kuma sakamakon da ta haifar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng