Ku yi amfani da makaman ku idan rayukan ku su na cikin hatsari - IGP (Bidiyo)

Ku yi amfani da makaman ku idan rayukan ku su na cikin hatsari - IGP (Bidiyo)

- Sufeta Janar, Adamu Mohammed ya ba wa 'yan sanda shawaran amfani da makamai don kare kansu idan akwai bukatar hakan

- Adamu Mohammed ya yi wannan bayani ne sakamakon hare-hare da bata-gari su ke kai wa 'yan sanda wanda ya janyo salwantar rayukan 'yan sandan da dama

- Ya kara da cewa, ko wanne dan sanda mutum ne kaman kowa wanda ke bukatar kare ransa

Sufeta janar na 'yan sanda Adamu Mohammed, ya shawarci 'yan sanda da su yi amfani da makamansu a duk lokacin da su ka fuskanci wani hatsari, jaridar The Nation ta wallafa.

Sufetan ya bayar da wannan shawara ne a 'yan kwanakin nan yayin da ya ke yin jawabi ga jami'an 'yan sanda. A halin yanzun, Adamu ya na tafiye-tafiye zuwa jihohi daban-daban domin duba irin barnar da bata-gari su ka yi ga hukumar ta 'yan sanda a lokacin zanga-zanga ta EndSARS.

Rahotonni sun nuna cewar 'yan sanda da dama sun rasa rayukansu, an kuma barnata ofisoshin na 'yan sanda masu yawa.

"Bai kamata abubuwan da su ka faru ga 'yan sanda da kuma ofisoshi na game da hari su hana mu fitowa don gudanar da ayyukan mu ba.

"Sai dai kuma ya zama dole mu kare kawunanmu a yayin sauke nauyin aikin na mu, don kuwa ko wanne dan sanda dan Adam ne wanda ke da hakkin tsira d rayuwarsa." In ji Sufetan

KU KARANTA: Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo

Ku yi amfani da makaman ku idan rayukan ku su na cikin hatsari - IGP (Bidiyo)
Ku yi amfani da makaman ku idan rayukan ku su na cikin hatsari - IGP (Bidiyo). Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: APC za ta fara yi wa mambobinta rijista a fadin kasar nan - Buni

A wani labari na daban, Sifeta janar, na 'yan sanda, Muhammad Adamu, ya ce kafafen sada zumuntar zamani su ne makaman da suka assasa rikicin EndSARS a jihohin Najeriya.

IGP din ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga gwamna Hope Uzodimma don yi masa jaje a kan asarar da masu zanga-zangar EndSARS suka tafka a jiharsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel