Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

- Masu garkuwa da mutane suna cigaba da cin karensu babu babbaka a titin Abuja zuwa Kaduna duk da yakarsu da ake yi

- A makon da ya gabata, sun sace yaron 'yar uwar tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi, mai suna Abdullahi, a hanyarsa ta komawa Kano kan titin Abuja zuwa Kaduna

- Wata majiya mai karfi ta ce sun gama tattara kudaden da masu garkuwa da mutanen suka bukata amma sun rasa lambar da za su kira su

Masu garkuwa da mutane sun sace 'dan 'Yar'uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda bayanai suka kammala, masu garkuwa da mutane sun sace Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba, a hanyarsa ta zuwa Kano a titin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Duk da dai ba a samu wani bayani daga 'yan sandan ba, wata majiya mai karfi ta ce basu so maganar ta fito waje ba.

KU KARANTA: Ku yi amfani da makaman ku idan rayukan ku su na cikin hatsari - IGP (Bidiyo)

Majiyar wacce take da kusanci da iyalin tsohon sarkin, ta ce masu garkuwa da mutanen sun tattauna da iyalin, inda suka nemi kudin fansa. Amma bai sanar da nawa suka bukata ba.

Yace iyalin sun tattaro kudaden amma sun rasa lambar da za su sanar da masu garkuwar, kuma har yanzu basu sake tattaunawa da su ba.

Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
Da duminsa: An sace dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Direbobin motocin haya masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna suna yawan korafi a kan yadda masu garkuwa da mutane suke tare mutane a hanyar.

A cewar direbobin, masu garkuwa da mutane sun fi tare mutane tsakanin 5 zuwa 7 na safe, da kuma 7 zuwa 9 na dare.

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamna Zulum ya bayyana hanya daya ta shawo kan Boko Haram

Sun bayyana cewa, 'yan ta'addan su na garkuwa da mutane duk lokacin da suka ga dama, wani lokacin su kan fake da zama direbobin motar haya.

Su na kwasar mutane su yi tafiyar a kalla kilo mita 30, sai su kai su wuraren da za a taresu, kamar yadda wani direba ya sanar.

A wani labari na daban, wasu malamai 5 da dalibi daya, sun kamu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare da ke jihar Legas.

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da hakan a ranar juma'a, jaridar The Punch ta wallafa.

Kamar yadda takardar mai taken jihar Legas ta tabbatar da samun wasu masu cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare kuma kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng