Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 5, sun ceto mata 3 da yara a Katsina

Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 5, sun ceto mata 3 da yara a Katsina

- Rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 5 a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina

- Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a Abuja, inda yace rundunar ta samu nasarar ceton mata 3 da yaransu

- Sai dai, daya daga cikin jaruman sojojin ya rasa ransa yayin kokarin ceton wata mata mai shayarwa, a cewar John Enenche

Rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

"Sai dai wani jarumin soja ya rasa rayuwarsa wurin kokarin ceto wata mata mai shayarwa," cewar Enenche.

KU KARANTA: An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi

Enenche ya ce rundunar ta samu nasarar kama wasu mutane 2 da ake zargin sun hada kai da wasu 'yan ta'adda da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, da wasu 'yan ta'adda 2 da ke karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 5, sun ceto mata 3 da yara a Katsina
Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 5, sun ceto mata 3 da yara a Katsina. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

"Ga dukkan alamu, sojojin Najeriya na iyakar kokarin ganin sun kawo karshen ta'addanci a Najeriya," a cewarsa.

Enenche ya ce ba kashe 'yan ta'addan kadai rundunar sojin take yi ba, ta samu nasarar amsar miyagun makamai da dama daga hannunsu.

KU KARANTA: Taron ASUU da FG: An tashi dutse a hannun riga, za a cigaba da yajin aiki

A wani labari na daban, a jiya ne CNG ta kushe taron da NGF suka yi a Kaduna, ta ce maimakon taron ya karkata matsalolin arewa kamar harkokin tsaro, rikicikin matasa, rashin ayyukan yi, talauci, harkar noma da tabarbarewar tattalin arziki, sai ya karkata a kan kananun matsaloli.

A wani taro da CNG tayi jiya a Kaduna, ta ce maimakon NGF ta mayar da hankali a kan manyan matsaloli, sai suka karkata a kan rikicin EndSARS da kuma matsalolin kafafen sada zumuntar zamani wanda hakan ba itace babbar matsalar arewa ba a yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel