Takunkumi a kan Musulmin duniya: Biden ya sha alwashin warwaresu a take

Takunkumi a kan Musulmin duniya: Biden ya sha alwashin warwaresu a take

- Zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin dakatar da dokar Trump ta hana musulmai da bakaken fata shiga Amurka

- Biden, ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin yayi adalci ga musulmai, wannan alkawarin nasa yasa musulmai da dama sun goya masa baya har ya samu nasara

- Dama tun hawan Trump mulki ya dakatar da kasashe kamar Iran, Libya, Somalia, Syria, Yemen, Najeriya, Sudan da sauran kasashe daga shiga Amurka

A ranar Joe Biden ta farko a kan karagar mulki, zababben shugaban kasar yayi niyyar soke dokar Donald Trump ta dakatar da matafiya daga kasashe 13, wadanda yawancinsu kasashen Afirika ne ko na musulmai.

Bayan hawan Trump karagar mulki a 2017, ya dakatar da matafiya musamman musulmai daga shiga Amurka, Aljazeera ta wallafa.

KU KARANTA: Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

Gwamnatin Trump, ta canja wasu dokokin kotun koli, inda ya kawo sababbin dokokinsa a 2018, inda ya canja yawancin kasashen da aka dakatar daga shiga Amurka.

Zababben shugaban kasar zai yi gaggawar canja dokokin, amma kotu za ta iya jinkiri.

A watan Oktoba, Biden ya yi alkawarin yin iyakar kokarinsa wurin yaki da ta'addanci.

Takunkumi a kan Musulmin Amurka: Biden ya sha alwashin warwaresu a take
Takunkumi a kan Musulmin Amurka: Biden ya sha alwashin warwaresu a take. Hoto daga @TheCable
Asali: Facebook

KU KARANTA: A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu

A cewarsa, "A matsayina na shugaban kasa, zan yi aiki tare da ku don yaki da tsana wacce take tsakanin al'umma. Mulkina zai yi iyakar kokarin ganin nayi adalci tsakanin musulmai da sauran 'yan Amurka.

"A ranata ta farko a karagar mulki, zan dakatar da hana musulmai walwala."

Dama Trump ya hana musulmai walwala, inda ya bayar da umarnin hana 'yan kasashe kamar Iran, Libya, Somalia, Syria da Yemen, wanda hakan ya jawo cece-kuce har ake ganin ya kyamaci addinin musulunci.

Daga baya, Trump ya kara fadada yawan kasashen kamar Venezuela da Korea ta arewa, daga baya ya hada da Najeriya, Sudan, Myanmar da wasu kasashe 3.

Mafi yawan kasashen musulmai sun kalli Donald Trump a matsayin mai kyamatar kasashen musulmai da kuma bakaken fata a mulkinsa.

A wani labari na daban, zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya mika sakon godiyarsa ga daukacin 'yan kasar Amurka saboda zabensa da suka yi don ya mulki kasar.

Biden mai cike da farinciki yayi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce zai mulki kowa cikin adalci, The Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel